A ranar 20 zuwa 21 ga watan gobe ne ake sa ran za a fara gudanar da gasar rukunin firimiya na Najeriya na bana. kungiyoyin 20 ne ake sa ran za su fafata a junansu inda daga karshe wacce ta zo ta daya za ta zama zakara.
A bara, kungiyar kwallon kafa ta Enyimba da ke Aba ce ta zama zakara bayan ta hada maki 70 sai ta biyu Warri Wolbes mai maki 66 sai kuma ta uku watau Nasarawa United wacce ta hada maki 63 yayin da Wikki Tourist da ke Bauchi ta kasance ta hudu da maki 63 amma Nasarawa United ta dara ta da yawan kwallaye.
Kano Pillars wacce ta zama zakara a shekaru uku a jere ta gama a matsayi na bakwai ne a jerin kungiyoyin da suka fafata a gasar a bara bayan ta hada maki 55.
Kamar yadda jadawalin da Hukumar shirya gasar ta kasa (NPFL) ta fitar an nuna kulob din Giwa FC zai fara kece raini ne da kulob din FC Ifeanyi Ubah sai Nasarawa United ta hadu da MFM FC sai kulob din Dolphins zai hadu da na Enyimba yayin da 3SC kuma za ta kece raini ne da Lobi Stars.
Sauran wasannin sun hada da Sunshine Stars za ta hadu da Akwa United yayin da Ikorodu United za ta hadu da Abia Warriors sai El-kanemi Warriors ta hadu da Wikki Tourist yayin da Heartland za ta hadu da Warri Wolbes.
Sauran wasanni su ne Kano Pillars da Enugu Rangers yayin da Filato United za ta kece raini da Neja Tornadoes.
kungiyoyin MFM Fc da na Ikorodu United su ne sababbin kungiyoyin biyu da suka samu nasarar haurowa gasar daga rukunin ’yan dagaji a bara.
Dukkan wasannin za su gudana ne a tsakanin ranakun 20 zuwa 21 ga watan Fabrairun, 2016.
20 ga Fabrairu za a fara gasar rukunin firimiya ta Najeriya
A ranar 20 zuwa 21 ga watan gobe ne ake sa ran za a fara gudanar da gasar rukunin firimiya na Najeriya na bana. kungiyoyin…