✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zan gaggauta sa hannu a rataye mai batanci ga Annabi —Ganduje

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya ce ba zai yi wata-wata ba wajen rattaba hannu a aiwatar da hukuncin rataya ga wanda ya yi batanci ga…

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya ce ba zai yi wata-wata ba wajen rattaba hannu a aiwatar da hukuncin rataya ga wanda ya yi batanci ga Annabi Muhammad (SAW).

Ganduje ya yi alkawarin sanya hannu a zartar wa matashin da ya aikata laifin Aminu Yahaya Sharif hukunci da zarar lokacin da kotu ta bayar na aiwatar da hukuncin ya yi.

“Kotun ta yi daidai wurin yanke hukuncin. An shaida mana cewa wanda ya aikata laifi na da kwana 30 da zai iya daukaka kara, idan bai daukaka ba kuma shi ke nan.

“Bayan sauraron malamai da masu ruwa da tsaki na Jiha, ba zan bata lokacin sa hannu a ka dokar zartar da hukuncin ba da lokacin ya kare ko Kotun Koli ta yanke hukunci”, inji gwamnan.

Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a taronsa da malaman addini da lauyoyi da sauransu masu ruwa da tsaki domin jin matsayinsu game da hukuncin kotun.

Idan ba a manta ba wata kotun Shari’ar Musulunci a Jihar Kano ta yanke wa wani matashi mai suna Aminu Yahaya Sharfi hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda yin batanci ga Manzon Allah (SAW) a wata waka da yi.

A dakaci karin bayani…