Atsi, ƙanwar Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ta rasu bayan samun raunin harbin bindiga da wani ɗan sanda ya yi mata.
Ko da yake ba a sanar da rasuwarta a hukumance ba, rahotanni sun ce ta rasu a wani asibiti da ba a bayyana sunansa a Abuja, inda ake duba lafiyarta bayan faruwar lamarin.
- Matashi ya daɓa wa mahaifiyarsa wuƙa a Bayelsa
- Dan Jam’iyyar LP a Majalisar Tarayya ya sauya sheka zuwa APC
Lamarin, ya faru ne a ranar 5 ga watan Disamba, lokacin da wasu mahara a kan babura suka kai wa tawagar motocin mahaifiyar gwamnan, Jummai Kefas, hari a kan hanyar Wukari-Kente a jihar.
Lokacin harin, wani ɗan sanda mai gadin tawagar ya yi ƙoƙarin harbin mahara da suka so tare hanyar motar da ke ɗauke da mahaifiyar gwamnan, amma harsashin ya samu Atsi, wadda ta ke zaune kusa da mahaifiyarta.
An garzaya da ita zuwa Asibitin Koyarwa na Wukari, amma daga baya aka tafi da ita Abuja domin ba ta kulawa ta musamman.
Wata majiya a gwamnatin jihar, ta tabbatar da rasuwarta, amma ta ce ba a sanar da labarin rasuwar a hukumance ba.