Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Besse/Maiyama daga Jihar Kebbi, Salisu Garba Koko, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Koko, ya sanar da wannan mataki ne cikin wata wasiƙa da ya aike kuma aka karanta a zauren majalisa.
- N50,000 aka biya ni don safarar harsasai zuwa Abuja – Matashi
- Noman rani ne zai kawar da yunwa a Yankin Tafkin Chadi — Zulum
Ya bayyana rikicin cikin gida a jam’iyyar PDP a matsayin dalilin da ya tilasta masa barin ta.
Wannan sauya sheƙa ya biyo bayan ficewar wani ɗan majalisar Kaduna, Amos Gwamna Magaji, wanda shi ma ya fice daga PDP sabida rikice-rikice.
Sai dai shugaban marasa rinjaye a majalisar, Kingsley Chinda, ya musanta zargin jam’iyyar na fama da rikice-rikice.
Ya jadadda cewar kowace jam’iyya tana da bambancin ra’ayi, amma hakan ba yana nufin samun rigingimu ba.