✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ɓacewar bindigogi 4,000: Sakaci ne dalili —’Yan sanda

Rundunar ta ɗora laifin ci gaban matsalar a kan abin da ta kira “sakacin” manyan jami’ai wajen tura ’yan sandan da ba su san ciwon…

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta ɗora laifin ɓacewar bindigo 3,907 a hannun jami’anta a kan sakaci da kuma ƙarancin iliminsu game da kula da makamai.

Da take ƙarin bayani kan yawaitar ɓacewar bindigon, rundunar ta ɗora laifin ci gaban matsalar a kan abin da ta kira “sakacin” manyan jami’ai wajen tura ’yan sandan da ba su san ciwon kansu ba wajen aiki.

Rundunar ta bayyana takaicinta ne a wata takardar cikin gida daga “TERROFOR ABUJA” wanda wakilinmu ya yi katarin samu a ranar Lahadi.

Takardar ta fito a yayin da Majalisar Dattawa take gudanar da bincike kan rahoton Babban Mai Binciken Kudi na Tarayya da ya nuna manyan bindigon ’yan sanda 3,907 sun ɓace.

A kan haka ne Kwamitin Majalisar mai kula da Kayan Gwamnati ya yi wa Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetekun da Mataimakin Sufeto-Janar mai Kula da Kuɗaɗe, Kasafi da Kayan Gwmanati, Suleiman Abdul, tambayoyin titsiye a kan ɓacewar bindigon.

Daga bisani kakakin rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya fito ya bayyana cewa ɓata-gari ne suka yi awon gaba da bindigogin da ake magana a kai.

Ya kuma yi zargin cewa akwai aringizo a adadin da rahoton Babban Mai Binciken Kuɗin ya bayar na bindigogin da suka ɓace.

Sai dai kuma a wani saƙon cikin gida da Rundunar ta aika mai lamba CQ: 2400/DOPS/ CTU/FHQ/ABJ/VOL. 10/90, zuwa wa rassanta, ta gargaɗi manyan jami’anta cewa za su yaba wa aya zaƙi idan suka sake irin haka ta ƙara faruwa a ƙarƙashin jagorancinsu.

Saƙon ya kuma umarci manyan jami’an rundunar da su riƙa bayar da rahoton duk makaman da ke ƙarƙashin kulawarsu kafin ko a ranar 23 na kowane wata.

Rundunar ta aike saƙon ne ga sassauta da ke Kano da Maiduguri da Legas da Fatakwal da Abuja da Aba da Warri da Damaturu, ta gargaɗi manyan jami’anta cewa za su yaba wa aya zaƙi idan suka sake irin haka ta ƙara faruwa a ƙarƙashin jagorancinsu.

Sauran su e: Bauchi, Enugu, Jos, Minna, Kano, Yola, Ibadan, Owerii Makurdi, Lokoja, Gusau, Gombe, Lafia, Ilorin, Yenagoa, Uyo, Okija, Kaduna da Uburu.