Gamayyar Kungiyoyin Ƙwadago da suka haɗa da Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya NLC da Ƙungiyar ‘Yan Kasuwa ta Kasa (TUC) sun ayyana shiga yajin aikin kwanaki 14 kamar yadda suka sanar da Gwamnatin Tarayya.
Yajin aikin kamar yadda sanarwar ta bayyana zai fara ne daga gobe Juma’a, 9 ga watan Fabarairu.
- Tsohon ɗan majalisa ya mutu yayin kallon wasan Najeriya da Afrika ta Kudu
- EFCC ta cafke kanin Hadi Sirika kan badakalar N8bn
’Yan Ƙwadagon dai sun zargi Gwamnatin Tarayya da gaza aiwatar da yarjejeniyar da suka ƙulla da ita tun a watan Oktoban bara.
‘Yarjejeniyar da gwamnatin Najeriya ta cimma da kungiyoyin kwadagon, ta kunshi inganta albashin ma’aikata, daidaita farashin man fetur da kuma shawo kan matsalar karyewar darajar kudin kasar wato Naira.
NLC da TUC sun ce, halin tsadar rayuwa da ‘yan Najeriya ke ciki abin dubawa ne matuka, amma sun ga alamun gwamnati ta yi biris da wannan matsala.
Hakan ta sanya ma’aikata a kasar suka yanke shawarar tafiya yajin aikin gargadi na tsawon makonni biyu, har zuwa lokacin da gwamnati za ta waiwaiyi ‘yan Najeriyar.