✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon ɗan majalisa ya mutu yayin kallon wasan Najeriya da Afrika ta Kudu

Tsohon ɗan Majalisar Tarayyar, Cairo Ojougboh ya mutu sakamakon bugun zuciya yayin kallon wasan Najeriya da Afrika ta Kudu.

Tsohon ɗan Majalisar Tarayya daga jihar Delta, Cairo Ojougboh ya mutu sakamakon bugun zuciya yayin kallon wasan Najeriya da Afrika ta Kudu.

Cairo Ojougboh ya yanke jiki ya mutu ne a daidai lokacin da za a yi bugun daga kai sai mai tsaron rago a wasan hamayya a gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON).

Marigayin ya kasance dan jam’iyyar APC ne kuma mai yawan babatu a kan batutuwan da suka taso a zauren majalisa.

Wasan Najeriya da Afrika ta Kudu, wanda a karshe Najeriya ta yi nasara, ya yi zafi sosai, kuma ya tayar da kura a soshiyal midiya.