✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Gwamnonin Arewa Suka Je Amurka Taron Tsaro

Gwamnonin Arewacin Najeriya da ake fuskantar kalubalen tsaro na kokarin lalubo ko ta wace hanya a samu dabarar dakile matsalar.

More Podcasts

Sauke Cikakken Shirin

Gwamnonin Arewacin Najeriya da ake fuskantar kalubalen tsaro na kokarin lalubo ko ta wace hanya a samu dabarar dakile matsalar.

Tafiyar gwamnoni 9 daga arewacin Najeriya zuwa Amurka a kwanan nan domin halartar taron tsaro ya nuna yadda suke kokarin daidaita lamarin har a matakin kasashen ketare.

Sai dai lamarin na zuwa ne a lokacin da wasu ke ganin an yi makamancinsa a Najeriya ba tare da halartar wani gwamna daga jihohin da suke fama da matsalar tsaron ba.

Shirin Najeriya a Yau ya duba tasirin da taron zai yi wajen magance matsalar yankunan.