✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ƙuncin rayuwar ’yan Najeriya ce damuwata, ba takarar 2027 ba

Atiku ya yi raddi ga tsohon Mataimakin Shugaban Jam'iyyar PDP na Ƙasa, Bode George, da ke neman ya haƙura daga takarar shugaban kasa a 2027

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, ya bayyana cewa halin ƙuncin rayuwa da ’yan Najeriya suke ciki a halin yanzu a mulkin Tinubu ne babbar damuwarsa, ba batun takarar zaɓen 2027 ba.

Atiku ya bayyana haka ne a martaninsa ga tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Bode George, da ke neman ya janye daga takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Sanarwar da kakakin Atiku, Paul Ibe, ya fitar, ya ce, “mu daina riga malam masallaci. A halin yanzu batun zaben 2027 ba ita ce a gaban Atiku Abubakar ba. Halin da ake ciki a 2024 ne damuwarsa.

“Ba 2025 ba ko 2026, ko ma gaba da nan ba, damuwarsa ita ce halin ha’ula’i da ’yan Najeriya suke ciki a halin yanzu sakamakon munanan manufofin gwamnati da rashin iya kamunn ludayinta.

“Duk wani ɗan Najeriya mafita yake nema daga bakin da Gwamnatin Tinubu ta jefa ƙasar.

“Don rashin tunani ne yanzu a fara batun takarar 2027 alhali wanda aka zaɓa a 2023 bai raunana komai ba, komai ya lalace a ƙasar.

“Ya kamata Bode George ya fara ba wa Tinubu shawara ya janye muggan manufofin gwamnatinsa da suka jefa al’umma cikin ƙuncin, ba batun takarar zaɓen 2027 ba.”

Aminiya ta ruwaito tsohon Mataimakin Shugaban PDP na Kasa, Cif Bode George, yana cewa takarar Shugaban Kasan 2027 a Jam’iyyar ta fi karfin Atiku Abubakar.

Bode George ya ce Atiku Abubakar bai dace ya fito a 2027 ba, kamata ya yi ya janye wa wani daga yankin Kudu mai jini a jika.

Wannan na cikin sanarwar da George ya fitar ranar Laraba, yana jaddada cewa wajibi ne dan takarar PDP a 2027 ya kasance daga yankin Kudu.

Dalili a cewarsa, shi ne, “saboda yanayin Najeriya da al’ummar kasar da kuma kundin tsarin mulkin PDP.

“A 2027 shekarun Atiku sun kai 81, don haka dole a lokacin dole ya yi koyi da Shugaba Joe Biden na Amurka, ya bar masu tasowa da jini a jika su shige ofishin shugaban kasa.

“Ba ni da wata matsala da Atiku, hasali ma abokina ne, amma idan gaskiya ta zole dole in fade ta; nan da 2027 shekarunsa sun haura 80.

“Ni dai da na haura shekaru 80, wane mulki ko mukami zan tsaya nema? Shi ma Atiku abin da ya kamace shi ke nan.

“Kwanan dai mun dai ga yadda Shugaba Joe Biden na Amurka ya janye wa mataimakiyarsa Kamala Harris, ta yi takarar shugaban kasa a babban zabe da ke tafe a watan Nuwamba.

“Hakan shi ne dattaku, kuma bin da ya kamata Alhaji Atiku Abubakar ya yi ke nan a 2027.

“Sai PDP ta tsayar da dan Kudu takarar kujerar shugaban kasa,” in ji George, wanda tsohon gwamnan Jihar Ondo ne a zamanin mulkin soja.