✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ƙudirin dawo da tsohon Taken Nijeriya ya samu goyon bayan Majalisar Tarayya

Dawo da taken zai tabbatar da muradan tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya da jaddada akidar kasa ɗaya al’umma ɗaya.

Ƙudirin neman Nijeriya ta koma kan tsohon takenta ya tsallake karatu na biyu a Majalisar Dattawa.

Ƙudirin da ɗaya daga cikin jagororin majalisar, Opeyemi Bamidele ya gabatar ya samu gagarumin goyan baya daga ’yan majalisar.

An mika ƙudirin zuwa ga kwamitocin majalisar kan Bangaren Shari’a da na Kare Hakkin Ɗan Adam da kuma na Harkokin Shari’a, inda aka buƙaci su dawo da rahoto a kansa cikin makonni biyu

’Yan majalisar waɗanda da alama galibinsu na goyon bayan ƙudirin, sun kafa hujja da cewar, tsohon taken zai ɗabbaƙa haɗin kai, zaman lafiya da bunkasar arzikin ƙasa, sabanin wanda ake amfani da shi a halin yanzu.

Bayan wata ganawar sirri da aka tafka muhawara akan ƙudirin, ’yan majalisar sun ce Taken Najeriyar da ake amfani da shi a halin yanzu gwamnatocin mulkin soja ne suka samar da shi ta hanyar irin nasu dokokin.

Don haka ’yan majalisar suka ce kamata ya yi a yi watsi da shi domin shigar da akidu da muradan tsarin dimokuraɗiyya Najeriya musamman ƙara jaddada akidar kasa ɗaya al’umma ɗaya.

An maye gurbin tsohon taken da ya soma da “Nigeria we hail thee” a Turance da wanda ya soma da “arise o’ compatriots” a shekarar 1978.

A wani labarin kuma, majalisar wakilai ta zartar da kudirin komawa kan tsohon taken na “Nigeria we hail thee.”

Cikin gaggawa Majalisar Wakilai ta yi wa ƙudirin karatu na 1 da na 2 da na 3 inda ta zartar da shi cikin ’yan mintuna.

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Farfesa Julius Ihonbvere ne ya jagoranci ɗaukar nauyin gabatar da ƙudirin da ya samu karɓuwa da gaggawa.

Ƙudirin ya tsallake karatu uku duk da cewa wasu ’yan majalisar — ciki har da Shugaban Marasa Rinjaye, Kingsley Chinda— sun nuna adawarsu ta komawa amfani da tsohon taken ƙasar.