✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abba ya mika wa Sanusi II takardar fara aiki

Gwamnan ya mika masa ne a bikin da aka gudanar ranar Juma'a a Fadar Gwamnatinn Kano.

Gwamna Abba Kabir ya mika wa Sarki Muhammadu Sanusi II takardar fara aiki a matsayin Sarkin Kano.

Gwamnan ya mika masa takardar aiki ne a wani takaitaccen biki da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Kano ranar Juma’a.

A jawabinsa na mika wa Sanusi takarda a ranar Juma’a, gwamnan ya ce, ba sabon sarki aka naɗa ba, “kujerarsa da ya tafi na wucin gadi ne yanzu muka dawo masa da ita.”

Sanusi ya ci gaba zama sarkin Kano ne shekara hudu bayan tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje ta tube shi a  2020.

An tube shi a lokacin ne shekara shida da hawansa kan karagar da marigayi Sarki Ado Bayero ya bari a shekrar 2014.

A lokacin ne gwamnatin Ganduje ta kirkiro tsarin masarautu biyar a jihar, ta kuma nada Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano.

A ranar Alhamis 23 ga Mayu, 2024, Majalisar Dokokin Kano ta kammala gyaran fuska ga dokar masarautun jihar, inda ta soke dukkan masarautun biyar da aka kirkiro a zamanin Ganduje.

A ranar ce Gwamna Abba ya rattaba hannu a bisa dokar ya kuma da ba wa sarakunanan masarautun wa’adin sa’a 48 su fice daga fada.