✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta dakatar da rushe masarautun Kano

Kotu ta hana gwamnatin Kano da jami'an tsaro amfani da sabuwar dokar masarauntun jihar wadda Gwamna Abba Kabir ya sanya wa hannu a ranar.

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta dakatar da tube sarakuna biyar da  rushe masarautunsu da gwamnatin jihar ta yi ranar Alhamis.

Mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman, ya kuma dakatar da gwamnatin Kano da jami’an tsaro amfani da sabuwar dokar masarauntun jihar wadda aka yi wa gyaran fuska, Gwamna Abba Kabir ya sanya wa hannu a ranar.

Umarnin wucin gadin dai ya shafi shugaban ’yan sanda da hukumar tsaro ta DSS da kuma Sibil Difens, har zuwa lokacin da za a kammala sauraron karar.

Sarkin Dawaki Babba Aminu Babba Danagundi, ne ya shigar da karar neman hana aiwatar da sabuwar dokar masarautun.

Sabuwar dokar ce ta kai ga dawo da Sarki Muhammadu Sanusi II a kujerar Sarkin Kano tare da kuma tsige Alhaji Aminu Ado Bayero da kujerar.

Hakazalika ta tube sarakunan sabbin masarutun Bichi, Gaya, Rano da Karaye wadanda tsohuwar Gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkiro a shekarar 2019.

Kotun ta ba da umarnin cewa ba za a yi amfani da sabuwar dokar masarautun da aka yi wa garan fsuka ba har sai ta kammala sauraron karar.

Wadanda ake kara sun ha da Gwamnatin Kano, majalisar dokokin jihar da shugabanta, da kuma hukumomin tsaro da sauransu.

A ranar Alhamis bayan sanya hannu a kan sabuwar dokar ce Gwamna Abba ya sanar da dawo da Sarki Sanusi II kan kujerar Sarkin Kano.

Gwamnan ya kuma ba wa sarakunan da aka rushe wa’adin sa’o’i 48 su fice daga fadar masarautun.