✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yi wa ilimi hidima yana faranta min rai — Kwankwaso

Tsohon gwamnan na Kano, ya ce zai ci gaba da yi wa ɓangarem ilimi hidima.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP kuma jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa gudunmuwarsa ga ɓangaren ilimi, shi ne abin da ya fi komai a wajensa a harkar siyasa.

Ya ce hidimta wa ilimi ya fi hanyoyi da gadajen sama da sauran ayyuka da ya yi a lokacin da ya mulki Jihar Kano.

Kwankwaso ya bayyana haka ne bayan buɗe sabon katafaren ɗakin taro a Jami’ar Skyline da ke Kano a matsayin wani ɓangare na murnar zagayowar ranar haihuwarsa, inda ya cika shekara 68.

Ya ce, “Abin da nake gani a matsayin gudunmawata ba su ne gadajen sama da titunan ƙasa ko hanyoyin kilomita biyar da na gina ba.

“Abin da nake gani a matsayin tubalina su ne Jami’ar Yusuf Maitama Sule da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Dangote da ke Wudil.”

Ya bayyana jajircewarsa ga cigaban ilimi, inda ya ce, “Ina so na tabbatar wa da mutanen Jihar Kano da Najeriya baki ɗaya cewa zan ci gaba da tallafa wa ɓangaren ilimi domin mu inganta rayuwar mutanenmu.”

Kwankwaso ya kuma bayyana irin jin daɗinsa na ganin yadda ayyukansa a ɓangaren ilimi ke tasiri ga al’umma.

Ya ce, “Ina matuƙar farin ciki idan na ga mutanen da suka amfana da abubuwan da muka yi sun zama manyan malaman da suke taimaka wa al’umma a yau.”

Ya nanata cewa ɓangaren ilimi zai ci gaba da kasancewa mafi muhimmanci a aikinsa.

“Zan ci gaba da tallafa wa ɓangaren ilimi a matakin digiri da sauransu domin wannan shi ne gado mafi tasiri da mutum zai bari a rayuwa.”

Kazalika, gidauniyar Kwankwasiyya ta ɗauki nauyin matasa 100 domin yin nazarin ayyukan jin-ƙai, yayin da gwamnatin jihar za ta horas da wasu matasa 150 kan kasuwanci da ƙere-ƙere.

Har wa yau, an zaɓi malamai 1,000 domin ba su horo kan ilimin kwamfuta.