✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zargin Kwartanci: Babu hujjar an yi zina — Jami’in Hisbah

Sai dai alƙalin kotun Musulunci ya bayar da umarnin gudanar da bincike.

Jami’in Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Malam Aliyu Dakata, ya ce babu wata hujja da ta nuna akwai alaƙa tsakanin Kwamishinan Jigawa da aka dakatar, Auwal Danladi Sankara da wata matar aure, mai suna Taslim Baba Nabegu.

A wata hira da ya yi da ’yan jarida, Dakata ya bayyana cewa Sankara bai aikata wani abu na rashin ɗa’a ba.

“Lokacin da muka isa wajen, mun tarar da Taslim a cikin motarta tana waya, yayin da Sankara ke tsaye a cikin filinsa da ake ginawa.

“Babu wata alama da ta nuna akwai mu’amala mara kyau a tsakaninsu,” in ji Dakata.

Jami’in na Hisbah ya musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta game da alakar cin amanar aure tsakanin mutanen biyu.

Idan ba a manta ba, an zargi Sankara da aikata baɗala da matar aure, wanda hakan ya sa gwamnan Jigawa ya dakatar da shi daga muƙaminsa.

A ranar Talata, lauyan Taslim, Barista Rabiu Shuaibu, ya ce ta rabu da mijinta tsawon watanni saboda cin zarafi.

“Sama da watanni 10 Taslim ta rabu da mijinta kuma tana gudanar da kasuwanci don tallafa wa ’ya’yanta.

“A ranar da abin ya faru, ta kai wa Sankara abinci ne, bayan ya yi oda, ba tare da sanin cewa mijinta yana bibiyarta ba,” in ji Shuaibu.

Sankara kuma ya ƙaryata zarge-zargen da ake masa, inda ya ce ba su da tushe kuma ba za su rasa nasaba da siyasa ba.

“Waɗannan zarge-zargen ba gaskiya ba ne kwata-kwata, an yi su ne don ɓata min suna.

“Ina girmama aure kuma ba zan taɓa yin abin da ake zargi na da shi ba. Wannan yunƙuri ne da gangan don ɓata min suna,” in ji shi.

Alƙalin Kotun Musulunci da ke Kano, Ibrahim Sarki Yola ya umarci Mataimakin Sufeton ’Yan Sanda na Shiyya ta Ɗaya, da ya gudanar da bincike kan lamarin.