Ƙungiyar Gwamnonin Arewa ta yi ta’aziyyar tsohon gwamnan farar hula na farko a Jihar Abiya, Cif Ogbonnaya Onu.
Shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewa 19, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ne ya miƙa ta’aziyyar a madadin mambobin ƙungiyar.
- Ina mai tabbatar wa Kotu cewa ni namiji ne — Bobrisky
- Kotu ta bayar da belin Emefiele kan Naira miliyan 50
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Babban Daraktan Yaɗa Labarai na Fadar Gwamnatin Gombe, Isma’ila Uba Misilli.
Gwamna Yahaya ya bayyana rasuwar tsohon Ministan Kimiyya da kirkire-kirkire a Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin babban rashi ga Nijeriya.
Sanarwar ta bayyana marigayin a matsayin Dattijon da ya bada gagarumar gudunmawa a fagen siyasar Najeriya, wanda ya yi riƙo da kyawawan ɗabi’u kuma ya yi aiki tuƙuru wajen hidimta wa ƙasa.
Gwamna Yahaya ya ce lokacin da Marigayi Onu ya yi Gwamnan Abiya da kuma lokacin da yake Ministan Kimiyya da kirkire-kirkire ya kasance mai sadaukarwa da gudanar da nagartaccen aiki da ya zama abun misali.
Kazalika, Gwamna Yahaya ya bayyana cewa marigayi Onu ya ba da gudunmawa sosai kuma ya taka rawar gani wajen ciyar da jam’iyyar APC gaba.
A ƙarshe sanarwar ta ce Gwamna Yahaya ya miƙa ta’aziyyar su ga iyalan Cif Ogbonnaya Onu, da gwamnatocin jihohin Ebonyi da Abia, da kuma ɗaukacin al’ummar Kudu Maso Gabas.
Ya kuma yi addu’ar Allah Ya jiƙan marigayin, ya kuma bai wa iyalan sa haƙurin jure wannan babban rashi.
Aminiya ta ruwaito, Mista Ogbonnaya Onu ya rasu ne a ranar Larabar da ta gabata yana da shekara 72 a duniya.