Tsohon Gwamnan Jahar Borno kuma tsohon Shugaban PDP, Ali Modu Sheriff ya tsallake rijiya da baya, a yayin wata ziyara da ya kai Jami’ar Amurka da ke Najeriya (AUN) a jahar Adamawa. Rohotanni sun bayyana cewa, tsohon gwamna ya ziyarci jami’ar ne domin ganin irin ababen da jami’ar ta kunsa, a inda aka fara hayaniya.
Kamar yadda rohoton ya nuna, an hango tsohon gwamnan ne a gaban dakin karatu na jami’ar, sai daliban makarantar suka shiga fada wa junansu cewa ai shi ne wadda ya kawo Boko Haram Maiduguri.
Kamar yadda majiyar da ta nema a sakaya sunaanta ta fada, ta bayyana cewa jim kadan bayan tsegumin da wasu daliban makarantar suka fara, sai wurin ya cika makil da dalibai, sai suka fara kiransa da ‘Boko Haram!’ ganin haka ya sanya aka yi maza aka sanya shi a motar da ke kusa da shi aka fitar da shi daga wurin.
Majiyar ta cigaba da cewa, ko da aka sanya shi a mota ba a tsaya a ko’ina ba sai a gidan Gwamnatin Adamawa domin kauce wa harin daliban. To amma da wakilinmu ya tuntubi mataimakin shugaban Jami’ar ta AUN ta fannin sadarwa, Farfesa Abba Tahir, ya karyata zancen, ya kuma shaida cewa ya san Modu Sheriff ya ziyarci jami’ar, amma babu abin da ya same shi.
Tsohon gwamnan ya ziyarci Yola ne domin daurin auren tsohon mai ba da shawara kan harkokin siyasa ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Ahmed Ali Gulak wadda a kwanan nan ya canza sheka daga PDP zuwa APC.
Koda manema labarai suka ziyarci Sheriff a masaukinsa na gidan gwamnatin jahar Adamawa domin jin bakinsa akan lamarin, ya ce shi dai ya kawo ziyarar sirri ne jahar kuma yana nan lafiya babu abinda ya same shi.