✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zuwa ga Gwamnan Jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso

Marubuci kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Malam Yasir Ramadan Gwale, ya rubuto wannan budaddiyar wasika zuwa ga Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Rabi’u…

Marubuci kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Malam Yasir Ramadan Gwale, ya rubuto wannan budaddiyar wasika zuwa ga Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso. Ga abin da yake cewa:
Assalamu Alaikum warahmatullah. Ina farawa da yi wa Allah godiya da Ya nuna mana samun habakar zaman lafiya a jiharmu ta Kano mai albarka.
Alhamdu lillah, muna yi wa Allah godiya, muna kuma rokon Allah Ya kara mana samun dawwamammen zaman lafiya a Jihar kano da kasa baki daya. Wadannan masu tayar mana da hankali babu sididi babu sadada, Allah Ka shirye su idan masu shiryuwa ne, idan kuma burinsu tayar da hankalin al’umma, Allah ka tozarta su, ka kumbura cikinsu, ka hana su samun abin da suka yi buri.
Bayan haka, ya mai girma Gwamna, ina son yin amfani da wannan dama domin na yi kira tare da roko ga wannan gwamnati taka, a kan a taimaka a sassauta dokar hana goyo a babur.
Ya mai girma Gwamna, hakika muna da masaniyar cewa wannan doka ta hana goyo a kan babur, an dauke ta ne da kyakykyawar niyya da kuma buri tare da fatan samun ingataccen tsaro a jiharmu mai albarka.
Ya mai girma Gwamna, muna masu roko a kan a sassauta wannan doka a kan kananan yara da kuma mata. Da yawan iyaye, musamman masu amfani da babura suna shan bakar wahala, musamman wajen jigilar ’ya’yansu zuwa makaranta. Mafiya yawancin masu amfani da babura daga cikin magidanta sukan so su kai yaransu makaranta a kan babur dinsu cikin sauki, amma a sanadin wannan doka ta sanya dole mutane sai dai su dauki hayar babur din A Daidaita Sahu wajen kai yaransu makaranta.
Hakika, da yawan magidanta aljihunsu yayi kuka ainun wajen biyan kudin A Daidaita Sahu, wanda in da an sassauta musu daukar yara, watakila su yi amfani da wannan rarar kudin wajen saya wa yaransu littattafai da takalman makaranta.
Haka kuma, wasu magidanta sukan buraci daukar iyalansu don kai su asibiti ko wata gajeriyar unguwa a bayan baburansu. Hakika da yawansu, su ma sun shiga cikin mawuyacin hali a sanadiyar rashin daukar iyalansu a bisa baburansu.
Allah Ya taimaki mai girma Gwamna, muna rokon alfarma, kamar yadda mun san kai mai kishin Kano ne da Kanawa. Hakika tarihinka ya nuna kana tausayin yara kanana da kuma mata da dattawa. Ya maigirma Gwamna, a taimaka a sassauta wannan doka a kan yara kanana da mata a cikin kwaryar birnin Kano.
Ya maigirma Gwamna, mun san da cewa a himmace kake wajen ganin ka hidimta wa al’ummar Jihar Kano ta kowane fanni, iyakar iyawarka. Don haka wannan ma wani aiki ne da daman can naka ne, na tausaya wa al’umma, musamman mata da yara kanana. Haka kuma, muna sane da yadda gwamnatinka ta himmatu wajen taimaka wa mata da kananan sana’o’i da jari wajen ganin sun taimaka wa yaransu. Wannan kam babu abin da za mu ce sai mu yi maka fatan Alheri. Allah Ya taimake ka.
Sannan kuma, ina kira tare da roko ga Gwamnatin Kano da masu hannu da shuni, a kan su kara himma wajen samar da karin ababen sufuri na zamani, wajen saukaka wa al’umma wahalar zirga-zirga, musamman irin manyan motocin nan na safa-safa masu iyakwandeshan cikin rahusa. Wanda muna sane cewa Gwamnati tana kokari a kan hakan, muna rokon a kara kokari.
Daga karshe, ya maigirma Gwamna, Ina rokon Gwamnatinka ta duba yuwuwar sassauta wannan doka a kan yara kanana da kuma mata. Haka kuma, mun gamsu da dukkan matakan da gwamnati take dauka wajen ganin an samu ingantaccen tsaro a ciki da wajen Jihar Kano. Allah Ya kara tabbatar mana da dawwamammen zaman lafiya a Jihar Kano da Najeriya baki daya.
Allah Ya taimaki Jihar Kano, Allah Ya taimaki Najeriya!
***
Haba Gwamnan Jihar Bauchi Isah Yuguda!
Shi kuwa Kabir Sakaina Layin ’Yangoro Malumfashi 08095968366, a nasa jan hankalin, Gwamnan Jihar Bauchi ya fuskanta da sakonsa, wanda ke cewa:
Na yi mamakin kalaman Gwamnan Jihar Bauchi, Isah Yuguda a kafafen watsa labaran kasashen waje (BBC, Jamus, Amurka da Radiyo Faransa), kan kokarinsa na kariya ga Arewa.
Acewar Malam Isah Yuguda, shi ba zai ci amanar Gwamnan Jihar Filato Jonah Jang ba kuma shi ba ya munafunci. Ya kuma kara da cewa kishin Arewa ne ya sa shi goyan bayan Jang. Abin tambaya ga Gwamna Yuguda shi ne, mene ne tsakaninsa da Janar Buhari da mutanen Bauchi da Atiku Abubakar da tsohon mataimakinsa Alhaji Garba Gadi a zaben 2007? Haka kuma mene ne tsakaninsa da Mataimakin Shugaban kasa Namadi Sambo da Jonathan a yanzu? Shin duk kishin Arewar ne ya sa shi mara wa Jonah Jang baya? Ko kuwa kishin Arewan ne ya sa shi yi wa Jonathan sharar hanyar sake darewa kan kujerar shugabancin kasar nan a 2015?
Daga karshe, zan so Malam Isah Yuguda ya lalubo inda kishinsa na Arewa ya makale lokacin karba-karba a 2011. Gaskiya dai daya ce, daga kin ta sai bata!
***
A hidindimun Gizagawa na makon nan kuwa, Gizagawan Abuja na sanar da taronsu da za su gudanar a jibi Lahadi, a inda suka saba taruwa, da misalin karge 1:30 na rana. Domin karin bayani, sai a tuntubi Idris Abubakar 08168170056
A labarin farin ciki kuwa, Bagizage Sunusi Isa Kwano zai yi aure a yau Jumu’a. Allah Ya ba da sa’a, Ya sanya arziki da albarka ga ango da amarya, amin.
Shi kuwa Ibrahim Maihoto 08187083387, karuwar haihuwar da namiji ya samu a Lahadi da ta gabata. Allah Ya raya, ya dayyaba, amin.