Mahauta a mayankar Abbatuwa ta Legas sun koka kan rashin ciniki lamarin da suka alakanta da tsadar shanu da kuma halin da ake ciki na hauhawar farashin kayayyakin masarufi.
Alhaji Garba A. Tanko, mahauci ne a Kasuwar Abbatuwa a Legas, ya shaida wa Aminiya cewa a tsawon shekara 28 da ya yi yana sana’ar fawa a Legas, babu lokacin da aka samu tashin farashin shanu kamar wannan lokaci.
- Naɗin sarautar Hausawa ta haddasa saɓani da fadar Oba na Benin
- Ƙyanda ta yi ajalin yara 19 a Adamawa
Ya ce tsadar ba ta rasa nasaba da cire tallafin mai da kuma hauhawar farashin kayayyaki.
“Lalacewar darajar Naira ta yi tasiri wajen tsadar shanu amma yanzu da darajar Naira ta fara farfadowa ana samun sauki kadan-kadan, fatanmu shi ne hakan ya dore domin a ci gaba da samun sauki ko Allah Ya sa kasuwar ta bude,” in ji shi.
Jibrin Muhammad Salisu, Shugaban Kungiyar Mahauta ta Amana ta kasuwar ya shaida wa Aminiya cewa ana samun saukar farashin sannu a hankali a kasuwar da kimanin kaso daya bisa goma, domin saniyar da ake sayar da ita Naira miliyan 1 da dubu 300, zuwa da dubu 400 a yanzu ana sayar da ita Naira miliyan 1 da dubu 250.
“Duk da saukar farashin da ake samu idan aka kwatanta da kwanakin baya amma babu ciniki, domin ana samun babbar saniya a kan Naira miliyan 1 da dubu 700, yayin da ake samun matsakaiciya a kan Naira miliyan 1 da dubu 100 zuwa Naira miliyan 1.
“Ko a jiya na yanka wasu manyan shanu da na saya a kan Naira miliyan daya da dubu 700, fatanmu shi ne Allah Ya kawo mana ciniki,” in ji Shi.
Shugaban Kungiyar Hadaka ta Mahautan Abbatuwa, Alhaji Abdullahi Ahmed, cewa ya yi, a yanzu ana samun sassauci inda farashin saniya ya ragu da kimanin Naira 50,000 zuwa Naira 100,000, ya ce amma duk da haka babu ciniki a kasuwar saboda tsadar rayuwa.
Shi kuwa sabon Sarkin Fawan Abbatuwar, Alhaji Bala Umaru cewa ya yi kasuwar za su samu daidaito domin ya shirya tsaf don tunkarar al’amuran da suke ci wa mahauta a Kasuwar Abbatuwa tuwo a kwarya.