✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliya: Zulum ya rufe makarantu nan take

Ambaliya ta sa Zulum ya rufe ɗauƙacin makarantun firamare da sakandare nan take

Gwamnan Borno, Babagana Zulum, ya rufe ɗauƙacin makarantun firamare da sakandare nan take sakamakon ruwan sama da albaliya mai ƙarfi.

Zulum ya umarci ma’aikatar ilimi ta rufe makarantun na tsawon makonni biyu, domin guje wa asarar rayukan dalibai a sakamakon ambaliyar a babban birnin jihar.

Wannan mataki na zuwa ne ranar Litinin da makarantu suka dawo daga hutun ƙarshen shekara domin fara zangon karatu na 2024/2025.

Kwamishinan Ilimin Jihar, Lawal Wakilbe ya shaida wa Aminiya cewa ana sa ran buɗe makarantun bayan makonnni, lokacin da ake fatan ambaliyar ta yi sauki.

Wakilbe ya ce daukar matakin rufe makarantun ya zama dole ne bayan zaman kwamitin da gwamnatin Zulum ta kafa domin taƙaita asarar rayuka a sakamakon ambaliya a jihar.

Ambaliya ta mamaye al’ummaomi da dama a kusan duk kananan hukumomin jihar.

Akasarinsu, musamman kananan Maiduguri, Jere da sauransu na fuskantar barazanar ambaliya mai karfi nan da awa 48 masu zuwa.

Kwamishinan ya ce ambaliyar ta zama babban ibtila’i a jihar inda ta raba dubban mutane da muhallansu

Gwamnatin Zulum ta kafa kwamiti karkashin sakataren gwamnatin jihar, Bukar Tijjani domin ɓullo da matakan gaggawa kan rage barnar ambaliyar da kuma bayar da dauki ga waɗanda abin ya shafa.