✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zulum ya roki sojoji su kafa sansanoni a dazukan Borno

Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya roki rundunar sojin Najeriya da ta kafa sansanonin soji na musamman a dajin Sambiza, Tsaunin Mandara, da Gudumbali…

Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya roki rundunar sojin Najeriya da ta kafa sansanonin soji na musamman a dajin Sambiza, Tsaunin Mandara, da Gudumbali da kuma Gabar Tafkin Chadi a yankin Marte, domin hana ’yan ta’adda sakat da kuma da maido da dawwamammen zaman lafiya a jihar na yankin Arewa maso Gabas baki daya.

Gwamna Babagana Zulum wanda ya yi wannan kiran a lokacin da kwamitin majalisar wakilai kan harkokin sojoji suka kai masa ziyarar ban girma a gidan gwamnati da ke Maiduguri, ya ce “idan jihar Borno ta samu tsaro sauran sassan kasar nan za a samu tsaro, a duk lokacin da rikici ya barke a Borno.  sauran sassan kasar nan za su kasance cikin rikici, ya kamata Sojoji su yi duk mai yiwuwa don tabbatar da tsaron Borno idan ba haka ba ba za a samu zaman lafiya a Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya ba”.

Ya kuma yaba wa Gwamnatin Tarayya da Hafsoshin Tsaro da Majalisar Dokoki ta kasa da suka dukufa wajen sayo wa sojoji makamai da jiragen yaki.

“Gwamna Zulum ya ce Borno na da isasshiyar kasar noma da idan aka yi noma yadda ya kamata za ta iya ciyar da al’ummar kasar nan baki daya.

 

“Don haka muna kira ga rundunar soji da ta kafa sansani a New Marte don tabbatar da aikin noma a bakin Tafkin Chadi.

“Hakan kan iya samar da karin filayen noma don samar da ayyukan yi da kuma wadatar da abinci da kuma tsaro da zaman lafiya a kasar.

“Borno wata kofa ce ta zuwa Chadi, Mali, Afirka ta Tsakiya wadda ke kawo saukin yaduwar kananan makamai; don haka sai mun tabbatar da Borno ta samu zaman lafiya sauran sassan kasar nan za su samu zaman lafiya.

“Dole ne mu magance tushen rikicin da ya hada da samar da filayen noma, saboda karancin abinci wanda shi ne mafi muni na rashin tsaro,” in ji Zulum.

Kwamitin Majalisar wakilai a kan sojoji karkashin ya je Maiduguri ne don duba yadda rundunar sojojin ke gudanar da ayyukansu da Kuma irin matsalolin su don magancewa.

“Muna samar da dokokin da suka dace don tabbatar da cewa Sojoji sun samu isassun kayan aiki don dawo da zaman lafiya a duk sassan kasar nan.

“Ina so in tabbatar muku cewa Majalisar Dokoki ta kasa za ta ci gaba da hada kai da tattaunawa da masu ruwa da tsaki don samar da mafita mai dorewa kan tsaro da kalubalen da ke damun al’ummar kasar,” in ji Shugaban.

Ya yi tsokaci kan Gwamna Babagana Zulum bisa yadda yake tallafa wa Sojoji da sauran jami’an tsaro domin samun zaman lafiya da jihar, ya kuma ba da tabbacin cewa majalisar za ta ci gaba da tallafa wa sojoji.