✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zulum ya raba wa ’yan gudun hijira Naira miliyan 200 a Bama

’Yan gudun hijira sama da dubu saba’in ne suka samu tallafin Naira miliyan 200 da kuma kayan abinci da Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno…

’Yan gudun hijira sama da dubu saba’in ne suka samu tallafin Naira miliyan 200 da kuma kayan abinci da Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya rarraba a garin Bama.

Gwamna Zulum ya rarraba tallafin ne a sansanonin ’yan gudun hijira biyar da ke garin Bama, inda kowane mutum ya samu kudi da kayan abinci da kuma karin atamfa ga mata.

Tun a Talatar da ta gabata ce Gwamnan ya kai ziyara garin Bama, inda ya yi kwana guda tare da bayar da umarnin gaggauta gina gidaje 500 a yankin Nguro Soye.

Kazalika, ya bayar da umarnin gida wasu karin gidaje 1,000 a garin wanda mayakan Boko Haram suka ruguza domin ganin mutanen da suka rasa muhallansu sun samu matsugunnai.

Aminiya ta ruwaito cewa Gwamnan ya raba wa mata 40,000 da maza 30,000 buhun sukari, shinkafa, kwalin taliya da kuma naira dubu biyar duk mutum daya.

Da yake jawabi, gwamnan jihar, ya ce gwamnatinsa na sane da halin da suke ci, sannan yana neman da su ci gaba da addu’o’in samun zaman lafiya mai dorewa a Jihar.

Babu shakka rikicin Boko Haram ya raba mutane da dama da muhallansu, sannan kuma ya sa sun rasa damar noma da kasuwanci na tsawo shekaru inda suka koma rayuwa a sansanonin ’yan gudun hijira da ke garin Bama