✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zulum ya raba wa ’yan gudun hijira N500m da kayan masarufi

Gwamnan Borno, Babagana Zulum, ya raba wa ’yan jiharsa mutum 5,000 da ke gudun hijira tallafin Naira milayan 500. Zulum ya raba tallafin ne bayan…

Gwamnan Borno, Babagana Zulum, ya raba wa ’yan jiharsa mutum 5,000 da ke gudun hijira tallafin Naira milayan 500.

Zulum ya raba tallafin ne bayan yi sammakon isa a sansanin da ke Maiduguri ne ranar Juma’a, inda mazauna sansanin da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu suka bayyana aniyarsu ta komawa garuruwansu.

Gwamnan ya shafe sama da awa bakwai yana rabon kayan tallafi inda “Aka ba wa kowane magidanci da matar da mijinta ya rasu N100,000 da kananan bukun shinkafa biyu da kwalin taliya da kuma jarkar man girki. 

“Matan aure kuma kowacce an ba ta N50,000, bayan an ba mazansu N100,000 da kayan abincin,” inji sanarwar da Gwamnatin Jihar Borno ta fitar.   

Zulum ya kai ziyarar ba-zatan ne domin samun ainihin ’yan gudun hijirar, saboda akwai masu yini a wurin, amma idan yamma ta yi, sai su koma cikin gari su kwana.

Gwamnatin jihar ce ta bayar da tsabar kudin, yawancin kayan abincin kuma tallafi ne daga Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar Raya yankin Arewa maso Gabas.

Zulum ya ce bayar tallafin ya zama dole saboda sansanin ya zame wa mutane mazauni, kuma yawancinsu sun dogara ne da kayan tallafi domin su rayu.

Sansanin ‘Bakassi Camp’, dai wasu kangayen gidajen gwamnati ne a kan titin Maiduguri zuwa Damboa inda a halin yanzu aka tsugunar da ’yan gudun hijira daga kananan hukumomin Monguno da Gwoza da Guzamala da Marte na Jihar Borno. 

Da yake sanar da aniyar gwamantin jihar ta rufe sansanin daga watan Disamba mai kamawa, gwamnan ya ce ba za a tilasta wa duk wanda ke son ci gaba da zama a wurin ya tashi ba.

Amma ya ce wadanda ke son su tashi su koma wasu wurare a jihar kuma za a ba su tallafi ta yadda za su ci gaba da rayuwa ba tare da sun dogara da kowa ba.