✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zulum ya raba wa ’yan gudun hijira N125.5m

Zulum ya yaba wa Shugaba Buhari kan taimakon Gwamnatin Jihar Borno.

Gwamnatin Jihar Borno ta tallafa wa mutum 40,000 da rikicin Boko Haram ya shafa a garin Damboa da kyautar kayan abinci da kudi miliyan N125.5.

Gwamna Babana Zulum ne ya jagoranci jami’an gwamnatin jihar zuwa Dambo, daga garin Chibok inda aka bude makarantar ’Yan Mata Chibok da Boko Haram ta sace dalibai 276 a 2014, da aka sabunta.

  1. An rufe Jami’ar KASU kan karin kudin makaranta
  2. Dakatar da Twitter: Najeriya ta gayyaci jakadun kasashen Yamma

Zulum da mukarraban nasa sun kwana a garin na Damboa inda suka duba wasu ayyukan tallafi da ci gaban al’ummar jihar.

A baya-bayan nan, rahotanni sun bayyana yadda sojoji suka fatattaki ’yan Boko Haram a Dambo.

A yayin ziyarar, an tallafa wa magidanta maza 14,900 da mata 25,100 wadanda yawancinsu rikicin Boko Haram ya raba da hanyoyin neman abincinsu.

Kowane magidanci ya samu buhun shinkafa, buhun masara, buhun wake; su kuwa mata kowacce ta samu tallafin N5,000 da turmin atamfa.

Da yake jawabi, Zulum ya ce kayan abincin na daga cikin tsarin Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar Shige da Fice ta Kasa.

Ya yi wa Shugaba Muhammadu Buhari jinjina game da irin goyon baya da yake ba wa Gwamnatin Jihar Borno.