Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya shafe tsawon ranar Litinin yana rabon kayan tallafi a garuruwan Ngoshe, Warabe da Pulka na Karamar Hukumar Gwoza da ke jihar.
A ziyararsa Ngoshe, Zulum ya kula da rabon kayan abinci da tabar kudi Naira miliyan 24 ga ’yan garin 1,200 da suka dawo daga gudun hijira daga Pulka da Maiduguri.
- Uwa ta rataye ’ya’yanta 2 don ta yi lalata da kare
- An ceto matar da ’yan uwanta suka kulle watanni 5 a daki
Kowane magidanci ya samu buhu mai nauyin kilogram 50-5- na masara da dawa, buhun wake mai nauyin kilogram 25, buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 12.5, jarkar man girki, sauran kayan hadin da kuma kudi N20,000.
Gwamnan ya ce za a ci gaba da tallafa wa al’ummomin zuwa lokacin damina wanda ake sa ran za su samu damar gudanar da ayyukan noma cikin aminci a gonakinsu domin ci gaba da rayuwarsu.
A ranar 15 ga watan Oktoba ne jama’ar Ngoshe da ke gudun hijira suka koma gidajensu bayan sojoji sun kakkabe yankin daga ragowar ’yan Boko Haram.
A ziyararsa zuwa garin, Zulum ya duba yanayin abubuwan more rayuwa da aka samar, sannan ya umarci Hukumar ba da Ilimin Bai-daya ta jihar (UBEC) ta hanzarta samar da kujeru da tebura tare da tabbatar da bude Makarantar Firamaren garin cikin mako biyu.
A halin yanzu an kammala kashi 95 cikin 100 na aikin makarantar.
Da yake duba cibiyar kula da lafiya ta garin, gwamnan ya umarci dan kwangilar da ya hanzarta kammalawa domin ma’aikatan lafiya su fara duba lafiyar al’ummar garin.
Daga nan ya ziyarci garin Warabe shi ma a Gwoza inda ya duba gidaje 350 da ake ginawa ga ’yan garin da kungiyar Boko Haram ta lalata gidajensu.
Zulum ya kuma ziyarci Pulka inda ya duba yadda ake gina babbar makarantar sakandare.