Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayar tallafin Naira miliyan 172 da kayan abinci ga mazauna Damboa 30,436.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Malam Isa Gusau ya fitar, Zulum da kansa ya shirya rabon kudade da kayan abinci ga al’ummar garin, ciki har da wadanda ambaliyar ruwa ta shafa.
- Ronaldo zai gana da sabon kocin Manchester United
- Najeriya ta ki amfani da sakamakon kidayar 2006 —Obasanjo
Gusau, ya ce an tantance mutum 436 wadanda suka rasa matsugunai sakamakon ambaliyar ruwa da aka yi a baya-bayan nan da ta yi sanadiyyar lalata gidaje da dama tare da raba wasu iyalai da muhallansu.
Bayan da shugaban karamar hukumar Damboa, Farfesa Adamu Aloma, ya shaida masa barnar da ambaliyar ruwa ta yi, Zulum ya bayar da umarnin a ba kowane daya daga cikin mutane 436 tsabar kudi har Naira 50,000, buhun Masara hade da kayan sawa.
Gwamnan, ya kuma jajanta wa wadanda abin ya shafa, sai dai ya bukaci mazauna yankin da su daina gina gidaje a kan magudanar ruwa domin gudun abin da zai iya faruwa a nan gaba.
Zulum ya kuma bayar da kyaututtukan da aka raba wa mutum 436 da ambaliyar ruwa ta shafa, ya kuma sa ido a rabon Naira 5,000 ga duk mutum daya da yadudduka ga mazauna yankin 30,000, wadanda yawancinsu zawarawa ne, mata masu rauni da maza daga al’ummomi daban-daban.
Gwamnan a ziyarar da ya kai yankin, ya kuma zagaya unguwannin Hausari da tsohuwar Kasuwar Damboa da Kachallaburari, tun bayan isarsa Damboa a ranar Lahadi.
Kazalika, Zulum ya ba da umarnin rarraba taraktoci ta hanyar tsarin rance ga manoma, yana mai cewa taraktocin za su kara habaka ayyukan noman ga mazauna yankin na Damboa.
A bangaren ilimi, Zulum ya duba hadaddiyar makarantar Islamiyya da ake ginawa domin koyar da ilimin addinin Islama da na boko a ciki.
Ziyarar dai ita ce ta kara kaimi domin bai wa matasan da suka halarci makarantun islamiyya na gargajiya da samun damar shiga manyan makarantu domin samun kwatankwacin takardar shaidar difloma.
Tuni dai gwamnan ya amince da gina makarantu makamancin haka a garin Monguno, bisa shirin samar da makarantun a daukacin kananan hukumomi 27 na Jihar Borno.
Idan aka yi la’akari da tarihin sama da shekara 1,000 na karatun addinin Musulunci, Borno tana da dubban mutane da ke da ilimin addinin Musulunci.
Makarantun Islamiyya mafi girma suna ba wa irin wadannan mutane, wadanda suka cika wasu sharuda, damar da za su iya samun damar shiga makarantun hadin gwiwa, inda suke samun kwatankwacin takardar shaidar difloma da za su iya neman karin ilimin boko a gaba.