✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zulum ya kai wa iyalan masuntan da ISWAP ta kashe tallafi

Gwamnati za ta ci gaba da bayar da taimako ga iyalan wadanda abin ya shafa.

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya kai ziyarar jaje da mika tallafi ga  iyalan masunta sama da 30 da ’yan ta’adda suka kashe ranar Laraba a kauyen Mukdolo da ke Karamar Hukumar Ngala.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, an kai wa masuntan hari ne yayin da Gwamna Zulum ya kai ziyara garin Dikwa, mai tazarar kilomita daya da kauyen da abin ya shafa.

Aminiya ta ruwaito cewa, ’yan ta’addan da ake zargi mayakan ISWAP ne masu ikirarin jihadi a Yammacin Afirka, sun yi wa fararen hular kwanton bauna ne yayin da  suka fita kamun kifi a Mukdolo.

Garin Dikwa wanda ke zaman shelkwatar Karamar Hukumar Dikwa, ya kasance tamkar cibiyar shiyyar Borno ta Tsakiya wanda a  shekarar 2014 kungiyar Boko Haram ta taba mamaye garin a matsayin tunga kafin sojoji su kwato shi kuma gwamnati ta sake gina shi gabanin dawowar mazaunansa.

Bayanai sun ce Gwamna Zulum ya gana da daukacin iyalan wadanda aka kashe na masunta a Fadar Shehun Dikwa, Alhaji Ibrahim Ibn Ibrahim El-Kanemi.

Da yake jawabi, Zulum ya ce “a madadin gwamnati da jama’a, na zo nan ne domin in jajanta muku kan kisan ‘yan uwanmu da suka je neman abin dogaro da kai,” in ji Zulum.

Ya kara da cewa, “ina rokon ku da ku yi tawassuli da Allah Madaukakin Sarki, domin Shi kadai ne zai iya daukar rai.  Muna addu’ar Allah Ya jikan su da rahama.”

Gwamna Zulum ya mika kayan agaji ga kowane iyalan da suka rasu don tallafa musu a lokacin zaman makoki.

Ya ba da tabbacin cewa gwamnati za ta ci gaba da bayar da taimako ga iyalan wadanda abin ya shafa.

A nasa jawabin, Mai Martaba Shehun Dikwa, Alhaji Ibrahim Ibn Ibrahim El-kanemi ya ce, a madadin iyalai da al’ummar da suka rasu ya nuna jin dadinsa ga Gwamna Zulum bisa wannan jaje da kuma tallafi da ya kawo wa iyalan wadanda abin ya shafa.