✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zulum ya bukaci makarantu masu zaman su taimaka wa habaka ilimi

Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya bukaci makarantu masu zaman kansu a jihar su ci gaba da bada tasu gudunmawar domin ci gaban…

Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya bukaci makarantu masu zaman kansu a jihar su ci gaba da bada tasu gudunmawar domin ci gaban ilimi musamman ilimin ’ya’ya mata, ganin koma-bayan da jihar ta samu a bangaren sakamakon  rikicin Boko Haram da ta shafe shekaru tana fama da shi.                                                                                                                                               Gwamnan ya yi wannan kira ne a wajen bikin cika shekara 20 da bude Makarantar Innobatibe da bude dakin taro na makarantar.

Gwamnan wanda Shugaban Hukumar Bada Ilimi Bai-Daya ta Jihar Dokta Kullima ya wakilta, ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da mara wa makarantu masu zaman kansu baya, don tallafa wa ci gaban ilimi, sannan ya hori makarantun su guji yin wani abu da zai kawo cikas ga kokarin da gwamnatin ke yi don habaka ilimi.

Gwamna Zulum ya yaba wa makarantar bisa hobbasar da take yi wajen bada ilimi ingantattace da kuma samar da dalibai hazikai da jihar take alfahari da su.

Da ya juya kan dalibai kuwa, Gwamnan ya yi kira gare su da su kasance masu himma wajen neman ilimin da zai kasance mai amfani ga al’ummar jihar da kasa baki daya.

A jawabin Kwamishinan Ilimi na Jihar Borno Malam Bello Ayuba yaba wa mai makarantar ya yi kan gudunmawar da take bayarwa ga ci gaban  ilimi, inda ya ce, “Samun irin wannan makaranta daga mace ’yar asalin Jihar Borno ba karamin ci gaba ba ne, ita ce  mace ta farko a nan jihar da ta bude makaranta mai zaman kanta.”

A jawabin Shugaban Kungiyar Iyayen da Malamai ta makarantar, Alhaji Bukar Audu ya bayyana farin cikinsa ganin yadda aka faro makarantar , amma ga shi yanzu sai yaye dalibai masu hazaka take ta yi, da ake alfahari da su a jihar da   wajenta. Ya ce wannan babban abin farin ciki ne, kuma ya yi kira ga iyaye su rika bada kula a kan karatun ’ya’yansu, musamman mata.

A jawabin mai makarantar Hajiya Amina Makintami ta gode wa Gwamnatin Jihar Borno kan goyon bayan da take ba makarantar.

An bada lambobin yabo ga fittatun ’yan asalin Jihar Borno uku da suka hada da Gwamna Babagana Umara Zulum da Hajiya Hafsatu Uwani, Babbar Magatakardar Kotun Koli, da marigayi tsohon Gwamnan Jihar Alhaji Mala Kachalla.

Wakilin Gwamnan ya bude babban dakin taron da aka sa wa sunan Alhaji Mala Kachalla.