Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya kaddamar da makarantar sakandare mai cin dalibai 1,500 a kauyen Buratai da ke Karamar Hukumar Biu ta jihar.
Zulum ya ba da umarnin daukar sabbin malamai 20 ’yan asalin kauyen a makarantar a matakin wucin gadi; wadanda ya ce yanayin hazakarsu za ta sa a dauke aiki na din-din-din.
- Babu mai hankalin da zai sake zaben APC a 2023 —Sanata Binos
- Ruwan sama da kankara ya lalata gonaki 300 a Katsina
Gwamnan ya kuma ba da umarnin gina gidaje 200 domin ’yan gudun hijira a kauyen Miringa da ke karamar hukumar.
Da yake jawabi, Kwamishinan Ilimi na Jihar Borno, Injiniya Lawan Abba Wakilbe ya ce a shekara uku da suka gabata Gwamna Zulum ya dauki malamai sama da 1,000, ba su horo da kuma tara su koyarwa a sassan Jihar Borno.
A cewarsa, gwamnan ya kuma gina katafarun makarantu 24 tare da gyara ajujuwa 600 a makarantu 100, baya ga kaddamar da gidajen malamai a garuruwan Maiduguri, Banki da Mafa.
Ya kara da cewa an gina bandaki guda 458 a makarantun firamare 350 a sassan jihar ta Borno.