✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zulum ya bai wa karamin yaro tallafin karatun N5m

Yaron ya yi amfani da laka wajen gina irin gadar sama da Zulum ya yi a Maiduguri

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum ya ba da tallafin Naira miliyan biyar ga wani yaro mai shekara1 3, Musa Sani, wanda ya yi amfani da laka ya kwaikwayi gadar sama ta farko a jihar, da gwamnan ya yi.

Zulum ya dauki nauyin karatun Musa ne zuwa wata makaranta mai zaman kanta, daga Golden Olive Academy, da ke Maiduguri, daga aji hudu na firamare zuwa kammala babbar sakandare.

Iyayen Musa talakawa ne da ke zaune a yankin unguwar Gwange a Jihar Borno kuma ya yi karatunsa har zuwa aji uku na firamare a makarantar Community da ke Gwange.

Kwanan nan Musa ya dauki hankalin Zulum bayan ya yi amfani da laka wajen gina irin gadar sama da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar a Maiduguri, a watan Disamba.

Zulum tare da Musa Sani

Gwamna Zulum ya yi mamakin hazakar yaron, inda ya saudu da iyayensa tare da ba shi tallafin karatu, don amfani da basirarsa.

Kan hakan ne gwamnan ya umarci Asusun Tallafawa Ilimi na Jihar Borno (ETF) da ya dauki nauyin karatun yaron.

Shugabar Hukumar ETF, Farfesa Hauwa Biu, ta gabatar da cekin N5,029,000, da kudin da aka riga aka biya wa wata makaranta mai zaman kanta da Musa ke karatu a yanzu.

Farfesa Biu ta gode wa gwamnan bisa wannan tallafi, sannan ta bukaci yaron da ya maida hankali kan karatunsa.