✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zuciyar mutum (7)

Idan muka tuna a makon da ya shige mun soma ganin cewa mutum ya rasa suturar da Allah Ya ba shi ne tun daga farko…

Idan muka tuna a makon da ya shige mun soma ganin cewa mutum ya rasa suturar da Allah Ya ba shi ne tun daga farko domin rashin biyayya, domin zunubi; da mtum ya ga cewa shi tsirara ne tare da matarsa, kuma ta shigo tsakaninsu, abin da ba su sani ba kafin aikata zunubin da suka yi; nan da nan suka soma neman yadda za su rufe wannan tsiraicin nasu. Da yake darajar Ubangiji Allah ta bar su, cikin tunaninsu na mutane, ganyen baure ne suka samo, suka dinka a madadin ainihin darajar da Allah Ya yi musu sutura da ita lokacin da Ya yi su. Mun san ganye ba zai dade ba zai bushe ya kuma kakkarye, a cikin yini daya dole ka yi ta canjawa- sau da dama, haka nan kuma za ka ci gaba da dinka sabon ganyen nan kana daurawa idan ba ka so ka zauna tsirara ka sha kunya. 

Me Allah Ya yi domin Ya magance wannan matsala ta rashin sutura?
Cikin alherinsa, Allah; koda yake bai ji dadin abin da mutum ya yi ba, sai ya yi musu sutura ta fata, “Ubangiji Allah kuma Ya yi wa Adamu da matarsa taggogi na fata, ya suturta su.” (Farawa:3:21).
Ina so mu gane wani abu mai muhimmanci, babu yadda za a samu fata muddin ba a kashe dabba ba, buba yadda za a kashe dabba ba tare da zubar da jinin dabbar ba, dole ne mu gane wannan domin nan gaba za mu san dalilin da ya sa muka samu ceta na har abada. Domin yadda zuciyar mutum ta cika da mugunta, har ya zo ga inda mutum ba zai yarda da laifinsa nan take ba, zai yi kokari ya kawo hujja ko kuwa dalilin da ya sa ya aikata abin da ya yi. Yawancin lokaci zai so ya dora wa wani laifin, mu lura da abin da Adamu ya gaya wa Allah lokacin da Ya zo wurinsu da maraice – “Sai suka ji muryar Ubangiji Allah tana yawo cikin gona da sanyin yamma: mutumin fa da matatasa suka buya daga fuskar Ubangiji Allah a cikin itatuwan gona. Ubangiji Allah kuma Ya kira mutumin Ya ce masa, ina kake? Shi kuwa ya ce na ji motsinka cikin gona, na ji tsoro, domin tsirara nake: na kuwa buya. Ya ce masa, wa ya fada maka tsirara kake? Ko ka ci daga itacen da an dokace ka kada ka ci? Mutumin ya ce, macen da Ka ba ni domin ta zauna tare da ni, ita ta ba ni daga itacen, ni kuwa na ci. Sai Ubangiji Ya ce wa macen, Mene ne wannan kaki yi? Macen ta ce, macijin ne ya rude ni, ni kuwa na ci.” (Farawa:3: 8 –13).
Ina so mu yi dan nazari kadan a wannan wurin. Da mutum ya gane cewa ya yi laifi, maimakon ya zo gaban Allah domin neman gafara, sai ya gwammace ya buya daga fuskar Allah. Haka yake ko a yau, duk mai aikata zunubi ba ya son zunubinsa ya fito fili, zai yi ta kokarin boyewa, domin ya san idan ya bari wadansu suka sani, zai zama masa da kunya; dole zai yi ta boye-boyen nan. Mutum har wa yau yana manta cewa, ba za a iya boyewa daga fuskar Allah ba. Duk abin da mutum zai yi, koda rami ne ya samu ya shiga kafin ya aikata wancan mummunan abu, yana sarari ne a gaban Allah, babu yadda mutum zai iya guje wa Allah. Abu na biye, shi ne – tun daga lokacin da mutum ya yi zunubi, ba ya so ya karbi laifinsa, sai dai ya dora wa wani.
Ubangiji Allah Ya tambayi mutumin a cikin aya ta 11 cewa: “…Ko ka ci daga itacen da na dokace ka kada ka ci?” Me ya kamata ya zama amsarsa? “Eh, ya Ubangiji Allah, na yi laifi, Ka yi mini gafara.” Amma abin da ya fadi shi ne: “Macen da Ka ba ni domin ta zauna tare da ni, ita ta ba ni daga itacen, ni kuwa na ci.” Abin da yake cewa shi ne “Allah, ba laifina ba ne, wannan matar da Kai Allah Ka kawo domin ta zauna tare da ni, ita ce ta ba ni, ni ban tsinko ’ya’yan itacen nan ba, ita ce ta kawo mini.” Haka ya so ya dora mata laifin. Lokacin da Allah Ya halicci wannan mata (Hauwa’u) ga abin da shi Adamu ya ce da ita: “…Mutumin kuwa ya ce, wannan yanzu kashi ne daga kasusuwana, nama ne daga namana, za a ce da ita mace, domind aga cikin namiji aka ciro ta.”(Farawa: 2 : 23). Lokacin da komai lafiya, yana jin dadi ya samu mataimakiya, yanzu da abu ya baci, yana so ya tura laifin ga Allah da matar, cewa yake yi idan ba don ka kawo wannan maatr ba, da ban aikata wannan zunubin ba. Allah sai Ya koma ga matar, ya tambaye ta ita ma: “Sai Ubangiji Allah Ya ce wa macen, Mene ne wannan kika yi? Macen ta ce, macijin ne ya rude ni, ni kuwa na ci.” (Farawa: 3: 13). Ita ma ta dora wa maciji laifi, babu wanda yana so ya dauki laifinsa har wa yau. daya daga cikin halayen da muka gada daga wurin iyayenmu na farko – son zargin wadansu a kan laifin da muka aikata. Sanadin wannan zunubi da suka yi, yau ya sa kowa ya gamu da shari’ar Allah. “Ubangiji Allah Ya ce wa macijin, tunda ka yi wannan, la’ananne ne kai cikin dukan bisashe da kowane dabba da rub-da-ciki za ka yi tafiya, za ka ci turbaya kuma dukan muddar ranka: tsakaninka da macen kuma zan kafa magabtaka da tsakanin zuriyarka da zuriyarta kuma, shi za ya kuje kanka, kai kuma za ka kuje duddugensa. Ya ce wa macen, zan yawaita bakin-cikinki kwarai da juna biyunki; da bakin ciki za ki haifi ’ya’ya, nufinki kuma za ya komo wurin mijinki, za ya kuwa shugabance ki. Kuma ya ce wa Adamu, don ka lura da muryar matarka, har ka ci kuma daga cikin itacen, wanda na dokace ka cewa ba za ka ci shi ba; saboda kai na la’anta kasa; da wahala za ka ci daga cikinta duk muddar ranka; kayayuwa da sarkakiya za ta haifa maka; ganyen saura kuma za ka ci; sai da jibi a fuskarka za ka ci abinci, har kuma ka koma kasa; gama daga cikinta aka ciro ka: gama turbaya ce kai, ga turbaya za ka koma.” (Farawa: 2 : 14 –19).
Idan muka duba a hankali, tun daga wancan lokaci, maciji – rub-da-ciki yake tafiya, kuma ya koma ga cin tabo/laka. Macen – Allah Ya yawaita bakin-cikinta da juna biyunta, kuma da bikin-ciki za ta haifi ’ya’ya. Shi mijin – Allah Ya la’anta kasa dominsa, zai sha wahala kafin ya samu abinci, Littafi Mai tsarki na cewa kasa za ta tsirar da kayoyi da sarkakiya a karshe kuma, mutum dole ya koma ga turbaya gama daga can ya fito. Wannan shari’ar Allah ta shafi kowane dayanmu.
Mene ne ya kawo mu ga wannan hali da muke ciki a yau? Zuciyar mutum wadda ba ta so ta yi biyayya ga umarnin Ubangiji Allah. Mu san cewa bai canja ba, kamar yadda ya shar’anta rashin biyayya a da, haka nan zai hukunta kowa da ya ki bin umarninSa.
Ba na so kowane dayanmu ya manta cewa zamanmu a wannan duniya, na dan lokaci ne kawai, dole za mu koma ga Allah. Ubangiji Allah Ya kara mana haskenSa, amin.