Mabukata 30,000 sun amfana da tallafin buhunan shinkafa da kamfanin Dangote ya raba a Jihar Osun.
Dangote ya ba da buhunan shinkafa masu cin kilogram 50 guda 6,000, wadanada aka raba wa mabarata, ’yan acaba da nakasassu da marayu.
Kowannnensu ya samu kilogram 10 na shinkafar attajirin da aka raba a fadin jihar domin rage musu raɗaɗin tsadar rayuwa.
Da yake sanya ido kan rabon tallafi shinkafar, shugaban al’ummar Musulmi ta jihar, Alhaji Mustafa Olawuyi, ya yaba wa kamfanin Dangote bisa wannan yunkurin.
- An ci gaba da shari’ar Bazamfariyar da aka kama da makamai a Kano
- An gurfanar da saurayi mai kai wa ’yan bindiga makamai a Kano
Ya bayyana cewa wuraren ibada da al’ummar Hausawa da Ibo da Fulani ma sun amfani da tallafin.
Alhaji Alhaji Mustafa Olawuyi ya kuma yi kira ga sauran mawadata da su yi koyi da Dangote wajen tallafa wa mabukata.