✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ci gaba da shari’ar Bazamfariyar da aka kama da makamai a Kano

Matar da ake zargi da safarar makamai ta zargi jami'an DSS da azabartar da ita da kuma tursasa mata cewa ta amsa cewa ita ce…

An ci gaba da shari’ar wata mata da aka kama da bindigogin harba rokoki guda uku a kusa da Kwalejin Horas da Kananan Hafsoshin yan Sanda da ke Wudil a jihar.

Hukumar DSS ce ta gurfanar da matar wadda yar asalin Karamar Hukumar Zurmi da ke Jihar Zamfara ce.

A zaman kotun na ranar Litinin, wadda ake zargin ta shaida wa kotu cewa tana tsaka da barci ne jami’an DSS suka je suka kama ta suka tsare ta.

A cewarta, jami’an hukumar sun azabartar da ita suka tursasa mata cewa ta amsa cewa ita ce mai makaman da ake zargi, amma ta ki amsawa.

Bayan sauraron bayanan ne kotu ta dage shari’ar zuwa ranar 24 ga watan yuni.