✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta karyata batun bude sansanin sojin kasar waje

Gwamnatin tarayya ta karyata ji-ta-ji-ta da ta ce ake yadawa cewa tana tattaunawa da wasu kasashen waje domin su bude sansanin sojinsu a Najeriya.

Gwamnatin tarayya ta karyata ji-ta-ji-ta da ta ce ake yadawa cewa tana tattaunawa da wasu kasashen waje domin su bude sansanin sojinsu a Najeriya.

Ministan yada labarai Mohammed Idris ya ce babu gaskiya a labarin karyan, don haka ya shawarci jama’a da su yi watsi da shi.

Ministan ya bayyana Najeriya ba ta irin wannan ganawa da kowace kasa ballantana wannan batu ya taso.

A sanarwar da ya fitar ranar Litinin, Ministan ya jaddada cewa babu kasar da ta yi wa gwamnatin Najeriya tayin bude sansanin sojinta a kasar, ballantana gwamnati ta saurare ta.

Ministan ya ci gaba da cewa duk da matsalolin tsaro da kasar ke fama da su, tana samun hadin kan da ya kamata daga kawayenta na kasashen waje kuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin cewa an shawo kan barazanar tsaron.