Amma Ubangiji Ya ga muguntar mutum ta yi yawa cikin duniya, kuma kowace shawara ta tunanin zuciyarsa mugunta ce kadai kulluyaumin.” (Farawa 6:5 ). “Zuciya ta fi komai rikici, ciwuta gare ta kwarai irin ta fidda zuciya; wa za ya san ta? Ni Ubangiji Mai bimbinin zuciya ne, ina gwada ciki, domin in saka wa kowane mutum bisa ga ayukansa, bisa ga ’ya’yan aikinsa.” (Irmiya 17: 9-10 ). “Mugun abu ke nan da ke akwaia cikin komai da a ke yi a duniya cewa, ga dukan mutane kadararsu daya ce: i ma, zuciyar ’yan Adam cike take da mugunta, hauka kuma tana cikin zuciyarsu muddar ransu, bayan wannan kuma sai su hadu da mutuwa.” (Mai-Wa’azi: 9:3 ). “Ya ce kuma, abin da ke fitowa daga cikin mutum, shi ke kazantar da mutum. Gama daga ciki, daga cikin zuciyar mutum, miyagun tunani ke fitowa, fasikanci da sata da kisan kai da zina da kwadayi da mugunta da ha’inci da mugun buri da maita da zage-zage da girman kai da wauta, duk wadannan miyagun abubuwa daga ciki suke fitowa, suna kazantar da mutum.” (Markus: 7: 20-23 ).” “Wanda ya dogara ga zuciyarsa wawa ne: Amma wanda ya taka a hankali, za a cece shi.” (Misalai: 28:26).
Lokacin da Allah Madaukakin Sarki Ya halicci mutum na farko a wannan duniya wato Adamu da Hauwa’u, bai halice shi da zuciyar mugunta ba ko kadan, abin da ya faru shi ne, lokacin da Allah Ya halice shi, sai Ya ba shi umarni ko doka wadda Ubangiji Yake so shi Adamu ya kiyaye ko kuwa ya yi biyayya gare ta. Adamu da matarsa Hauwa’u suka soma bin umurnin Allah yayin da suke cikin gonar adnin. “Ubangiji Allah kuwa Ya siffanta mutum daga turbayar kasa, Ya hura masa numfashin rai cikin hancinsa; mutum kuma ya zama rayayyen mai rai. Ubangiji Allah kuma Ya dasa gona daga wajen gabas, a cikin Adnin; can kuwa Ya sanya mutumin da ya siffanta. Kowane itacen da ke mai sha’awar gani, mai kyau kuwa domin ci, Ubangiji Allah Ya sa ya tsiro daga kasa; itacen rai kuma a tsakiyar gona, da itacen sanin nagarta da mugunta…………..Sai Ubangiji Allah Ya dauki mutum, Ya sanya shi a cikin gonar Adnin ya aikace shi, kuma ya tsare. Ubangiji Allah kuma Ya dokaci mutumin, Yana cewa, “An yarda maka ka ci daga kowane itacen gona a sake: amma daga itace na sanin nagarta da mugunta ba za ka diba ba ka ci: cikin ranar da ka ci, mutuwa za ka yi lallai.” (Farawa:2:7-9, 15-17) Wannan shi ne mafarin mutum wanda ba shi da zunubi ko kadan. Mutun yana rayuwa ta wurin numfashin rai da Allah da kanSa Ya hura a cikinsa. Idan da mutum ya yi biyayya ga dokar Ubangiji, da mutum ya ci gaba da yin biyayya ga muryar Allah da har yau muna cikin jin dadin da mutum ya soma ji a cikin gonar Adnin. Abin kaito shi ne mutum bai ci gaba da jin tsoron Allah ya yi miSa biyayya ba. Maimakon haka sai mutum ya saurari muryar Shaidan wanda aikinsa shi ne ya rudi mutane su yi wa Allah rashin biyayya. “Amma maciji ya fi kowane dabba da Ubangiji Allah Ya yi hila. Ya fa ce wa macen, ashe, ko Allah Ya ce ba za ku ci daga dukkan itatuwa na gona ba? Sai macen ta ce da macijin, daga ’ya’ya na itatuwan gona an yarda mana mu ci, amma daga ’ya’yan itace wanda ke cikin tsakiyar gona, Allah Ya ce, ba za ku ci ba, ba kuwa za ku taba ba, domin kada ku mutu.” Sai macijin ya ce da macen, lallai ba za ku mutu ba.”
Ina so mu lura, Allah da kanSa Ya ce “a ranar da ka ci mutuwa za ka yi lallai.” Mene ne ma’anar kalmar nan lallai? -ma’anarta: babu shakka, tabbatacce. Allah Ya ce a ranar da Adamu ya ci daga wannan itacen sanin nagarta da mugunta, a ranar zai mutu, sai Shaidan ya zo ya ce “lallai ba za ku mutu ba.” Abin da Shaidan yake yi a kullum ke nan, yana gaba da maganar Allah a koyaushe da yake Allah Ya gama shar’anta shi, aikin da ya sa a gaba ke nan, ya nuna wa Allah taurin kai; Shaidan sai ya ce wa macen: “Gama Allah ya sani ran da kuka ci daga ciki, ran nan idanunku za su bude, za ku zama kamar Allah, kuna sane da nagarta da mugunta.(5)” Shaitan gwani ne in ya zo ga yaudara, makaryaci ne shi, ba shi iya fadin gaskiya ko na anini, haka ya faru “sa’anda macen ta lura itacen yana da kyau domin ci, abin sha’awa ne kuma ga idanu, itacen kuma abin marmari ne domin bada hikima, sai ta diba yayansa, ta ci; ta kuma ba mijinta tare da ita , shi kwa ya ci”(6). Tun daga wancan lokaci, mutum ya shiga wahala domin rashin biyayya ga umarnin Allah; wannan shi ne ainihin zunubi wanda ya kawo mutum cikin wahalar da duk duniya take fuskanta a yau.” Dukansu biyu idanunsu suka bude, suka waye kuma tsirara ne su; suka daddauki ganyayen baure, suka yi wa kansu mukuru.” (7).
Mutuwar da Ubangiji Allah ke nufi a nan ita ce mutuwar ruhi ko kuwa rabuwa da Allah. Mutane da dama yau sun bar Shaidan ya yaudare su, musamman in ya shafi kwadayin kayan duniya wadda ba ta dauwama; mu tuna ba yanzu ya soma ba, a’a tun daga wancan lokacin ne mugunta ta shigo zuciyar kowane dan Adam a duniya, kowane mutum kuma ya zama mai zunubi, kasasshe a gaban Allah. “Amma Ubangiji Allah Ya ga muguntar mutum ta yi yawa cikin duniya , kuma kowace shawara ta tunanin zuciyarsa mugunta ce kulluyaumin.” (Farawa:6:5). Ba nufin Allah ba ne mutum ya gaji irin wannan zuciya wadda take cike da mugunta. Yau idan aka haifi yaro, ba sai ka koya masa yin mugunta ko zunubi ba, haka kawai idan ka bar shi ya girma yadda ya ga dama, zai nuna halin mugunta ne da kuma halin rashin jin tsoron Allah; yin abin da zai gamshi Allah abu ne wanda sai mun sa kai mun koya ko an karantar da mu.
Tun daga lokacin da mutum ya yi laifi a gaban Allah, mutum ya rabu da ganawa da Allah, domin Allah Shi Mai tsarki ne babu kazanta a tare da Shi ko kadan, Shi ba Mai zunubi ba ne kamar Iblis, domin haka ne babu yadda zai yi zumunci da mutum wadda Ya halitta.
Zamu so mu yi kokarin bincike daga Littafi Mai tsarki don gane abubuwa game da zuciyar mutum;
Mene ne zuciyar mutum? Ya ya zuciyar mutum take yin aiki? Wane irin shiri ne Ubangiji Allah Ya yi domin Ya taimaki zuciyar mutum?
Ina fata Allah cikin alherinSa zai taimake mu idan Ya bar mu cikin masu rai zuwa lokaci na gaba. Mu kuma ci gaba da yin addu’a muna rokon Allah Ya taimake mu musamman a wannan mawuyacin zamani da muke ciki. Allah Shi kadai ke da ikon kawo mana salama a wannan kasa tamu ba mutum ba. Bari Ubangiji Allah Ya ci gaba da tsare mu.
Za mu cigaba