✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zlatan Ibrahimovic ya yi ritaya daga tamaula

Lokaci ya yi na bankwana da buga kwallon kafa baki daya.

Tauraron kungiyar AC Milan, Zlatan Ibrahimovic ya sanar da yin ritaya daga kwallon kafa.

Zlatan ya sanar da matakin ne a ranar Lahadin nan da ta gabata, bayan wasan karshe na kakar wasa ta bana da kungiyarsa ta AC Milan ta buga.

Yayin wasan na gasar Serie A, AC Milan ce ta lallasa Verona da 3-1 a filin wasanta na San Siro, inda a nan ne Ibrahimovic ya ce lokaci ya yi na bankwana da buga kwallon kafa baki daya.

Dan wasan dai na daga cikin ’yan gaba da suka fi yin fice wajen mallakar basirar sarrafa kwallon kafa tamkar masu sihiri a duniyar tamaula, abin da ya sa shi zama daga cikin mafi kwarewa da aka taba gani a tarihin kwallon kafa.

Zlatan Ibrahimovic

Ibrahimovic mai shekaru 41 a yanzu, ya lashe kofuna 34, da kuma cin kwallaye 570 a matakan kungiyoyi da na tawagar kasarsa, a tsawon lokacin da ya shafe yana haskawa a fagen kwallon kafa.

A kungiyar Malmo FF a kasar ta Sweden cikin shekarar 1999, dan wasan ya fara buga wasa a matakin kwararru, bayan shekaru biyu kuma ya kulla yarjejeniya da Ajax, daga nan ne kuma ya koma Juventus, sai Inter Milan, kana Barcelona a shekarar 2009.

Daga Spain Ibrahimovic ya sake komawa Italiya, inda ya kulla yarjejeniya da AC Milan daga bisani kuma ya koma PSG a shekarar 2012.

Ragowar kungiyoyin da Ibrahimovic ya buga wa wasanni sun hada da Manchester United da LA Galaxy ta Amurka, kafin ya sake komawa AC Milan inda nan ne yayi ritaya.