Manyan ’yan siyarar Najeriya akalla 58 sun kashe daruruwan miliyoyin Naira domin kai wa Uban Jam’iyyar APC na Kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ziyara a kasar Birtaniya.
Bincike ya gano cewa ’yan siyasar da suka niki gari musamman domin zuwa ganin Tinubu a birnin Landan sun kashe akalla Naira miliyan 265.
- ’Yan sanda sun kwato mutum 187 daga hannun ’yan bindigar Zamfara
- Shin za a hana yara mallakar waya a Najeriya?
Tsohon Gwaman Jihar Sakkwato, Aliyu Magatakarda Wamakko; tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Abudlazeez Yari da tsohon Gwamnan Borno, Sanata Kashim Shettima da daga cikin wadanda suka niki gari takanas, domin ganin Tinubu a Landan.
Tinubu, wanda mai fada a ji ne a jam’iyyar APC mai mulki, ya yi akalla wata uku a Landan, inda yake jinya bayan an yi masa tiyata a gwiwa.
A ranar 12 ga watan Agusta, 2021, Buhari ya je ya duba shi, lokacin da Buharin ya je Landan ganin likita.
Tun bayan lokacin ’yan siyasa ke ta tururuwar ziyartar Tinubu a Landan, inda har yanzu yake ana yi masa gashin kafa.
Gwamnoni da ’yan majalisar tarayya da na jiha da tawagogi na musamman an ci gaba da tafiya takanas domin zuwa dubiyar da ake ta ce-ce-ku-ce saboda makudan kudaden da ziyarar tasu take lakumewa.
Baya ga matsayin Tinubu a APC, ana hasashen zai fito neman kujerar shugaban kasa a jam’iyyar a zaben 2023; Ana kuma tsegumi cewa sun kulla yarjejeniya cewa shi Buhari zai ba tikitin tsayawa a zaben da ke tafe.
-
– Gwamnonin da suka ziyarci Tinubu
Daga cikin gwamnonin da suka niki gari don ganin Tinubu har da Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas — inda Tinubu ya fito — da Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya koma Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi.
Sauran su ne Gwamna Rotimi Akeredolu na Ondo da Dapo Abiodun na Ogun; sai kuma Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a lokacin da ya je bikin yayen dansa daga jami’a a kasar Birtaniya.
A lokacin dubiyar da Ganduje ya je an gan shi tare da dan autan nasa, Muhammad da kuma ’yan Majalisar dokoki biyu: Kabiru Alhassan Rurum and Aminu Babba Dan’Agundi tare da Tinubu.
-
– Sanatoci da tsoffin gwamnoni
Kawo yanzu, tsoffin gwamnoni hudu — uku daga cikinsu sanatoci — ne suka ziyarci Tinubu a Landan, ciki har da tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata Aliyu Wamakko.
Sauran su ne Sanata Ibikunle Amosun na Jihar Ogun da Sanata Kashim Shettima daga Jihar Borno da kuma Abdulaziz Yari na Jihar Zamfara.
Sanatocin da suka ziyarci Tinubu a Landan on hada da Sanata Abu Ibrahim da Mohammed Sani (Neja ta Gabas) da Sanata Tokunbo Abiru (Legas ta Gabas).
Sai Santa Opeyemi Bamidele (Ekiti ta Tsakiya); Sanata Adeola Solomon (Legas ta Tsakiya) da Sanata Adelere Oriolowo (Osun ta Yamma).
-
Wase ya jagoranci tawagar ’Yan Arewa
A baya-bayan nan ne kuma ’yan Arewa a Majalisar Wakilai suka tura tawaga ta musamman mai mutum 20, karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar, Ahmed Wase, suka je takanas ta Landan domin duba Tinubu.
Tawatar ta kunshi Shugaban Masu Rinjaye, Alhassan Ado-Doguwa; Honorabul Abubakar Fulata; Shugaban Kwamitin Soji, Abdulrazak Namdas; Honorabul Blessing Onuh daga Jihar Binuwai; ’yar tsohon Shugaban Majalisar Dattawa David Mark; Sada Soli daga Katsina, Abubakar Lado Suleja daga Jihar Neja wa wasu mutum 13.
Honorabul Usman Zannna ma na daga cikin wadanda suka ziyarci Tinubun a can Birtaniya.
Shi ma Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, ya je dubiyar uban gidansa, Tinubu, tare da hadimansa wadanda su ne ’yan rakiyarsa.
-
– Tawagar ’yan majalisa da gwamnati
Kazalika Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Legas, Mudashiru Obasa da dan Majalisar Wakilai Honorabul James Faleke mai wakiltar mazabar Ikeja ta jihar.
Bayan ziyarar da dubiyar Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya kai wa Tinubu a Landan, Gwamnatin Jihar Legas ta tura tawaga ta musamman domin duba shi.
Tawagar ta kunshi Mataimakin Gwamnan Jihar Legas, Obafemi Hamzat; Shugaban Ma’aikata, Tayo Ayinde; da mataimkinsa, Gboyega Soyannwo da Mashawarcin gwamnan kan Ilimi, Tokunbo Wahab.
-
– Shugabannin siyasa
Tsohon Mashawarci kan Harkokin Shari’a na APC na Kasa, Muiz Banire (SAN); Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomi ta Najeriya (ALGON); Adekunle Akanbi; da tsohon sakataren ALGON na Jihar Legas, Rasaq Ajala su ma sun je.
Shugaban Karamar Hukumar Isolo ta Jihar Legas, Otunba Adebayo Olasoju, da ’yan majalisar dokokin jihar – Temitope Adewale (Ifako-Ijaiye 1); Nureni Akinsanya (Mushin 1); Sylvester Ogunkelu (Epe 2); duk sun je.
Suran masu ziyarar sun hada da Majalisar Mashawartan Gwamnan Jihar Legas da suka hada da Sanata Anthony Adefuye, Mista Wale Edun da Misis Idiat Adebule, — tsohuwar mataimakiyar gwamnan jihar.
-
– An kashe N265m
A cikin ’yan siyasar 58 da suka ziyarci Tinubu a Landan, Buhari da Ganduje da wasu mutum uku ne kadai wani abu na kashin kansu ya kai su Landan amma suka biya suka ziyarci Tinubu.
Ragowar mutum 53 kuma sun niki gari ne musamman domin zuwa su gan shi a can.
Masu harkar sufurin jiragen sama sun kiyasta cewa abin da kowane daya daga cikin mutum 53 din ya kashe a ziyararsa zuwa Birtaniya a babbar kujera ko matsakaiciya, zai kama daga Naira miliyan hudu zuwa biyar.
Jimillar kudin da ’yan siyasar suka kashe ya kama Naira miliyan 265 ke nan, duba da yadda farashin tikitin jirgi ke ta hauhawa.
-
– Nawa kowa ya kashe?
Kudaden da suka kashe ya kunshi kudin tikitin jirgi, da na masauki da abinci da saurasnu.
Bayan da muka samu daga kamfanonin sufuri da yawon shakatawa sun nuna kudin dakin otal da suke kamawa a Landan ya kai wa Fam 150 zuwa fam 200 (wato N90,000 zuwa N120, 000) a kullum.
Kudin tikitin jirgin kamfanfin British Airways daga Najeriya zuwa Landan kai tsaye a babbar kujera kuma Dala 7,000 (Naira milyan hudu, a kafan farashin Dala N570) ne zuwa Dala 10,000 (Naira miliyan 5.7).
Kujera matsakaiciya kuwma Dala 4,000 ne zuwa Dala 6,000 — ya danganci lokacin da mutum ya kama kujera.
-
– Kudin wa aka kashe a ziyarar?
Duk da cewa, Tinubu dai ba jami’in gwamnati ba ne, ana zargin cewa ’yan siyasar da ke ziyartar sa na amfani ne da kudaden gwamnati.
Wani mai sharhi kan al’amaran yau da kullum, Kwamred Toyin Raheem, ya ce duk da cewa yin ziyarar dubiya ba laifi bane, yawancin masu zuwa ganin Tinubu na amfani ne da kudaden gwamanti.
Raheem, wanda shi ne Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Yaki da Rashawa da Mummunan Shugabanci (CACOBAG), ya ce maimakon ziyarar, abin da ya fi dacea shi ne a yi amfani da kudaden wajen samar wa mutane ababen more rayuwa.
“Ziyarar dubiya ba laifi ba ne amma ba da kudin gwamnati ya kamata a yi ba. Yawancin masu zuwa ziyarar na amfani ne da kudaden gwamnati ba kudaden aljihunsu ba.
“Shi ma nauyi yana daga cikin aikin da aka zabe su su yi ne? Ga ayyuka birjik da ke bukatar a yi wu, a ayyukan samar da abubuwan more rayuwa barkatai ba su yi ba, amma suna kashe kudade wajen ziyartar shugabansu na siyasa. Da kudinsu ya kamata su yi ba da kudin gwamnati ba,” a cewarsa.
Shugaban Cibiyar Yada Labarai da Wayar da Kai ta Afirka, (AFRICMIL), Dokta Chido Onumah, ya ce ko an tambayi masu zuwa ganin Tinubu da kudin gwamnati musantawa za su yi.
“Amma manuniya ce game da dabi’ar shugabanninmu na siyasa da yadda suke fifita kansu a kan rayuwar al’umma.
“Abin takaicin shi ne yadda shugabannin da suka samu damar kyautata rayuwar al’umma ba sa ganin dacewar su inganta bangaren kiwon lafiya a kasar nan,” kamar yadda Dokta Onumah ya bayyana.
A nashi bangaren, Shugaban kungiyar da ke bibiyar yadda ake kashe kudaden gwamnati domin tabbatar da ci gaba (CODE), Hamza B. Lawal, ya ce “Sanin kowa ne cewa ba daidai ba ne amfani da kudaden gwamnati ta irin wadannan tafiye-tafiye.
“Abin tambaya shi ne, me ya kawo hakan? Rashin bibiya ne da kuma rashin hukunci”
-
– ‘Da kudin aljihunmu muka je’Da u
Mun tuntubi gwamnatin jihar Legas domin jin wanda ya dauki nauyin tafiye-tafiyen dubiyar da aka yi zuwa Landan domin ganin Tinubu.
Sakataren Yada Labarn Gwamnan Jihar Legas, Gboyega Akoshile, ya ce mutanen da suka kai ziyarar sun yi amfani ne da kudadensu.
Daya daga cikin ’yan majalisa da suka ziyarci Tinubu, Abubakar Lado Suleja, ya ce kowannensu ya kashe kimanin Naira miliyan 1.2 a ziyarar da zuka kai wa tsohon gwamnan na Jihar Legas.
“Kowa da aljihunsu ya je. Mu da kanmu muka sayi tikitin jirgi muka kama masauki; Babu wanda ya dauki nauyinmu. Haba!
“Haba! Yanzu dan majalisa ba shi da kudin zuwa Landan ya yi kwana uku zuwa biyar ke nan? Kowannenmu da kudinshi ya je,” kamar yadda ya bayyana a ranar Alhamis.
Shi masa kakakin Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai, Muhammad Puma, ya musanta cewa ubangidnsa, Ahmed Idris Wase da sauran ’yan tawagarsa sun yi amfani da kudaden gwamnati domin ziyartar Tinubu a Landan.
Puma, wanda ya ce zargin abin dariya ne ya kara da cewa, “Shin dan majalisa ba shi da karfin aljihun zuwa kasar Birtaniya ke nan? Ni ina ganin wannan maganar bai ma kamata ta taso ba”.