✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ziyarar wanda ya kai cutar Kurana Legas ta sa an killace kamfani a Ogun

Gwamnatin jihar Ogun ta killace katafaren kamfanin siminti na Lafarge da ke yankin Ewekoro a jihar, bayan da gwamnatin tarayya ta tabbatar da bullar cutar…

Gwamnatin jihar Ogun ta killace katafaren kamfanin siminti na Lafarge da ke yankin Ewekoro a jihar, bayan da gwamnatin tarayya ta tabbatar da bullar cutar Koronar a Legas.

Kwamishinar kiwon lafiya na jihar Ogun Dakta Tomi Coker, ne ta sanarwa ‘yan jaridu hakan ranar Juma’a, ta ce dan kasar Italiya da ya shigo da cutar Korona Najeriya kwararre ne da ke yi wa kamfanin simintin Lafarge aiki a matsayin Mashawarci ga kamfanin, kana ya ziyarci kamfanin a ranar Talatar da ta gabata.

Bayan ya nuna alamun kamuwa da zazzabi aka kwantar da shi a karamin asibitin da ke cikin kamfanin simintin kafin daga bisani aka garzaya da shi Legas bayan da cutar tayi kamari a ranar Laraba.

Ta ce, za a bibiyi duk wadanda mutumin ya yi mu’amala dasu a kuma killace su har tsawon akalla kwanaki 14.

A jihar Legas ma gwamnatin jihar ta dukufa wajen lalubo daukacin mutanen da suka hadu da dan kasar Italiyar a lokacin shigowarsa Najeriya, mutanen da suka hadar da wadanda suka shigo jirgi tare da ma’aikatan da suka tarbe shi, tare da ma’aikatan da ke aiki a tashar jirgin sama dana kula da shige da fice wato ‘Immigration’ da ma’aikatan hotal din da ya yi amfani da su a lokacin da ya isa Legas.

Kwamishinar kiwon lafiya ta jihar Ogun Dakta Tomi Coker