Bayan shan ce-ce-ku-ce kan zargin masu shara a Jihar Kano na cewa gwamnatin ta riƙe musu alawus ɗinsu, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba da umarnin a biya su cikin gaggawa.
Abba ta wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya umarci ma’aikatar muhalli da kula da tsafta (REMASAB) ta tabbatar da biyan duk wasu kudaden alawus-alawus na masu shara da suka gada daga gwamnatin da ta gabata.
Baya ga haka, Gwamnan ya ƙaryata jita-jitar shirin gwamnatinsa na korar ma’aikatan, ya ce ba shi da niyyar hana ma’aikatan da ba su yi laifin komai ba abin dogaro da kai.
- Sun yi wa wata tsirara suka yada bidiyon a soshial midiya
- Yadda sojoji suka aika ’yan ta’adda lahira a Borno da Neja
Gwamnan ya bayar da wannan umarni ne a ranar Lahadi yayin wata ganawa da wakilan masu sharar a gidan gwamnati.
Ya nuna rashin gamsuwa da jinkirin biyan wasu kuɗaɗe bayan amincewarsa.
A cewarsa, “Ban ba da umarnin korar wani daga cikinku ba, maimakon haka ma, mun ɗauki karin ma’aikatan ne domin muhallanmu su kasance cikin tsafta.
“A matsayinmu na ’yan ƙasa na gari, wace fa’ida zan samu kuma wane daɗi zan ji idan na sallame ku daga abin da kuke yi kuke samun abincin yau da kullum?
“Wannan taron ya zama wajibi bisa la’akari da kukan da ake yi a kai a kai da kuma labaru marasa daɗi da nake samu saboda rashin biyan ku alawus-alawus din ku.
“Ina mai tabbatar muku da cewa za ku karɓi alawus dinku nan ba da jimawa ba, mun gano inda matsalar take kuma mun gano yadda za mu kawo karshenta”
Gwamnan ya bayyana shirin gwamnatinsa na sayo manyan motoci masu ɗauke da kayan aiki na zamani (Bocket lifters) domin sauƙaƙa kwashe sharar ba kawai daga tituna ba har ma daga lunguna da saƙunan jihar.