✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda sojoji suka aika ’yan ta’adda lahira a Borno da Neja

A rana guda jiragen soji suka yi luguden wuta a kan maboyan mayakan Boko Haram da ’yan bindiga a dazukan jihohin Borno da Neja

Rundunar Sojin Saman Najeriya ta ce ta hallaka ma’yakan Boko Haram da ’yan bindiga a jihohin Borno da Neja a makon da ya gabata.

Daraktan yaɗa labaran rundunar, AVM Edward Gabkwet ya bayyana cewa aikin sojojin saman na kara da dakile ’yan bindiga da masu tada ƙayar baya daga kai hare-hare a yankunan ƙasar nan.

AVM Gabkwet ya ce a ranar 3 ga watan Mayun nan ne rundunar ta kai wani mummunan hari kan maɓoyar ’yan ta’addar da ke Chinene a cikin duwatsun yankin Mandara.

A bayanin nasa, ya ce sun hango tankokin yaƙi kimanin guda bakwai a ɓoye a ƙarƙashin wasu bishiyoyi.

Sanarwar ta ce ranar ce kumar rundunar ta ka hari hari kan wasu ’yan bindiga da ke addabar al’ummar yankin Allawa da ke kusa da Shiroro a Jihar Neja.

Gabkwet ya ce a samu nasarar kai waɗannan hare-hare ne sakamakon amfani da bayanan sirrin da suka samu.

A ranar 1 da watan Mayu ne aka samu labarin cewa wasu yan ta’adda ɗauke da muggan makamai sun kai hari ƙauyen Allawa, inda suka kashe da dama suka kuma saci kayan amfanin yau da kullum.