Hukumar Gidan Waya ta Najeriya (NIPOST) ta fara kaddamar da yaki da masu safarar kayayyaki marasa lasisi a Jihar Kaduna.
NIPOST na kai samame ofisoshin da ke gudanar da irin waɗannan sana’o’i ba bisa ƙaida ba ne tana tare rufe su.
Babban Manajan NIPOST, Sashen Kula da Kayayyaki da Ayyuka (CLRD), Mista Shonde Dotun, ya ce masu irin wannan aiki ba bisa ka’ida ba ne ke kara ta’azzara ƙalubalen tsaron da ake fama da shi a ƙasar nan.
Ya ce wasu ma’aikatan kamfanonin suna safarar makamai da muggan kwayoyi, wanda hakan ke kawo barazana ga tsaro a Najeriya.
Dotun ya ce, “Bincike ya nuna cewa mutane da yawa suna wannan aikin ne ba tare da lasisi kamar yadda dokar NIPOST ta wajabta ba.”
Ya nuna damuwarsa kan yawaitar ma’aikata marasa lasisi masu aikata miyagun laifuka kamar zamba cikin aminci da safarar haramtattun kayayyaki.
“Wasu daga cikinsu sun shiga harkar ne da zuciya biyu. Wasu ba su da ofisoshi, wasu kuma suna yaudarar mutane ne.
“Wasunsu ana amfani da su wurinn safarar makamai da kwayoyi.
“Mun kama wasu daga cikinsu dauke da daloli, wasu da hodar iblis a cikin burodi, wasu dauke da tabar wiwi a ƙunshe cikin mutum-mutumi.”
Mista Shonde Dotun Ya bayyana cewa, a shekarar da ta gabata kadai, an kama masu safarar miyagun kwayoyi 500 acikin masu irin wannan sana’a, kuma an gurfanar da su a gaban kuliya.
A wannan aiki da aka fara faro daga Jihar Kano a kwanan nan an kama sama da mutane 100.
Irin masu wannan sana’a dai sune waɗan da ke karɓar saƙonni daga wuri zuwa wuri akan babura wasu kuma a motoci a cikin birane.