Majalisar Tarayya ta shiga tsakani a rikicin harajin kan sarki da ya barke tsakanin hukumomin tara kudaden shiga na tarayya.
Rikicin ya kunno kai ne bayan hukumar tara kudanen shiga ta kasa (FIRS) ta zargi hukumar gidan waya ta kasa (NIPOST) da bude asusun ajiyar kudaden ba bisa ka’ida ba.
“A matsayin kwamitin lura da hukumomin kudi, mun kira ku ne mu gani ko kuna bin doka”, inji Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai, James Faleke.
A zaman tattaunawan kwamitin da hukumomin kan kudin shiga biliyan N58, Faleke ya ce surutan da hukumomin ke yi babban abun kunya ne.
Zaman ya samu halarcin shugaban NIPOST, Ismail Adebanjo da Shugabar Kwamitin Amintattun hukumar Maimuna Yahaya Abubakar da wasu manyan jami’ai.
Yayin jawabi a kan kan N58 na harajin da aka tara daga watan Fabrairun 2016 zuwa Afrilun 2020, shugaban FIRS Muhammad Nami ya ce suna tara Naira biliyan uku na harajin kan sarki a duk sati daga bankuna kasuwanci.
Rikicin harajin kan sarkin ya taso ne a ‘yan makonnin nan bayan hukumomin sun fara cacar baki kan wane ne a cikinsu ke da hakkin tarawa.
FIRS ta zargi NIPOST da bude asusun ajiyar harajin a Babban Bankin Najeriya (CBN) ba bisa ka’ida ba, da yunkurin facaka da kudaden.
NIPOST ta karyata zargin ta kuma ce ba ta da ikon taba kudaden.
Ta kara da cewa an bude asusun ne da sanin CBN tun lokacin da CBAN ya umarci bankuna su rika cire harajin kan sarki na N50 daga wurin masu ajiya.