✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gidan Malam Shekarau ya yi gobara

Dakuna 10 da dukiyoyi sun kone a gobarar gidan tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau da ke unguwar Mundubawa

Gobara ta tashi a gidan tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau da ke unguwar Mundubawa.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta ce dakuna shida da suto biyu da dakunan girki biyu da bandakuna sun kome kurmus a gobarar.

Bayan samun nasarar kashe wutar, kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta Saminu Yusif Abudullahi, ya ce wutar ta yi barna sosai a gidan.

Jami’in ya ce, “hukumarmu na gudanar da bincike domin gano musabbabin tashin goabarar, amma mazauna gidan sun alakanta ta da matsalar wutar lantarki.”

Ana zargin gobarar ta daren Lahadi ta fara tashi ne a daga dakin girki sannan ta bazu zuwa wasu sassan gidan, inda aka yi asarar dukiya mai tarin yawa.