Shugaban Matasan APC na unguwar Herwagana a Jihar Gombe, Shafi’u Idris ya bayyana cewa ziyarar da dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Gombe da Kwami da Funakaye a majalisar Tarayya, Hon. Yaya Bauchi Tongo, ta haifar da rudani.
Shafi’u Idris, ya bayyana hakan ne a Gombe a lokacin da yake zantawa da Aminiya, inda ya ce tunda Yaya Bauchi, ya ci zabe ya guje wa jama’ar mazabarsa ya fake da sunan yana shari’a a kotu, bai zuwa Gombe balle ya taimaki jama’a, sai yanzu da ya ga siyasa ta fara matsowa sannan ya san mutane na da muhimmanci bayan ya guje su.
Ya ce shin Yaya Bauchi ya manta ne kan yadda ya raba kan jama’ar mazabar Gombe da Kwami da Funakaye, sannan kuma ya gaza kawo musu ayyukan raya kasa, shi ne zai zo yana cika bakin cewar ya shekara biyu yana shari’a, bayan shekara daya ya yi, wanda ma ya shekara uku daga jihar Neja ya taimaki jama’ar sa balle shi.
“Yaya Bauchi a zuwan da ya yi a makon da ya gabata ya raba motoci ga shugabanin APC na kananan hukumomi biyu na Gombe da Funakaye ya hana na Kwami, shin da haka za mu sake zabarsa? Yaya Bauchi bai san siyasa ba, da dan siyasa ne da ba zai butulcewa
‘ya’ya da shugabanin APC na karamar hukumar Gombe da suka ba shi kuri’u dubu 69 da 300 ba.
Daga nan sai ya ce idan jimawa ana shari’a ne bai kai dan majalisar
Jihar Neja, Lado Suleja ba, wanda yake wakiltar Tafa da Gurara da Suleja, shi shekara uku ya yi yana fama a kotun shari’a amma ya taimaki jama’arsa. Sannan sai ya ce Yaya Bauchi, ya sani ba zai yiwu ya sake yiwa mutane dodorido wajen yin amfani da su dan ya ci zabe ba, yanzu lokacin guguwa ta wuce kyan mutum ne zai kai shi ga cin zabe.