✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zikiri abincin zukata (1)

Masallacin Annabi, Madina Fassarar Salihu Maqera Huxuba ta Farko:Godiya ta tabbata ga Allah Mai girma a cikin qudirarSa, Mabuwayi a cikin qarfinSa, Masani ga halin…

Masallacin Annabi, Madina

Fassarar Salihu Maqera

Huxuba ta Farko:
Godiya ta tabbata ga Allah Mai girma a cikin qudirarSa, Mabuwayi a cikin qarfinSa, Masani ga halin bawa a voyensa da bayyanensa. Ina gode maSa-Maxaukaki-kuma ina yi maSa shukura a bisa ximbin ni’imarSa da falalarSa. Na shaida babu babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kaxai ba Ya da abokin tarayya a gare shi, tsayuwa bisa ga zikirinSa. Kuma na shaida lallai Shugabanmu Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa, wanda aka aiko don yi wa Allah xa’a a tudunSa da tekunSa. Tsira da Amincin Allah su qara tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa da masu bin su da kyautatawa matuqar gira-gizai suna zuwa da xigon ruwa, da aminci, aminci mai yawa.
Bayan haka, ina yi muku wasiyya-da ni kaina- da bin Allah Maxaukaki da taqawa: “Ya ku waxanda suka yi imani! Ku bi Allah da taqawa a kan hakkin binSa da taqawa, kuma kada ku mutu face kuna masu sallamawa (Musulmi). (Al’Imrana: 102).
Ya bayin Allah! Allah Ta’ala Ya ce: “Ya ku waxanda suka yi imani! Ku ambaci Allah, Ambato mai yawa. Kuma ku tsarkake Shi, a safiya da maraice.” (Ahzab: 41- 42).
Musulmi yana samun xaukaka ta hanyar tsarkake zuciyarsa, kuma sha’aninta a wurin Ubangijinta ya girmama ta hanyar ambaton Allah Mauxaukaki. Zikirin Allah shi ne abincin zukatan mutane, wanda idan suka rabu da shi, sai zukatansu su zamo kamar qaburbura. Zikiri ne ke raya gidanjensu wanda idan aka yi wasa da shi, sai su zamo kufai. Shi ne makaminsu da suke yaqar masu tare hanya. Kuma shi ne ruwansu da suke kashe gobara da shi, shi ne maganin cututtukansu wanda idan suka rabu da shi sai zukatansu su karaya, da shi ake kawar da bala’o’i kuma baqaqen ciki suke gushewa. Idan bala’i ya lulluve su zuwa gare shi suke fakewa, idan abubuwa marasa daxi suka sauko musu gare shi suke kokawa. Shi ne dausayin Aljannarsu da suke jujjuya a cikinsa, shi ne jarinsu da suke kasuwanci da shi, yana jawo zuciya zuwa ga dariya da farin ciki, ya shayar da ita farin ciki da annashuwa. Yana saukar da natsuwa a majiyoyi, ya sa harsuna su kurumce (daga jin haram da lagawu) ya sa idanunwa su makance daga (kallon haram), da shi Allah Yake ado ga zukatan masu zikiri kamar yadda Yake ado da shi ga gannan masu kallo.
Alhasan Basri (Allah Ya yi masa rahama) ya ce: “Ku nemi xanxanon (zaqin imani) a cikin abubuwa uku: A cikin Sallah da Zikiri da Karatun Alqur’ani. Idan kuka samu madallah, idan ba ku samu ba, to qofa ta rufe muku,”
Malik bn Dinar (Allah Ya yi masa rahama) ya ce: “Masu jin daxi ba su ji daxi da wani abu kamar zikirin Allah ba, babu wani abu mafi sauqi kamarsa kuma mafi zaqi kuma mafi jawo farin ciki da sanya zuciya farin ciki kamarsa.”
Mafi girman masu zikiri shi ne Manzon Allah (SAW), ba ya rabuwa da ambaton Ubangijinsa, ba ya yankewa daga yi maSa xa’a kuma ba ya natsuwa da waninSa. Idan ya ambaci Allah sai zuciyarsa ta yi khushu’i, qirjinsa ya yi laushi, jikinsa ya raurawa, hawaye ya kwarara. Ya ce ga Ibn Mas’ud (RA): “Ko za ka karanta min (Alqur’ani)?” Sai na ce: “Ya Manzon Allah, in karanta maka, alhali kai aka saukarwa?” Ya ce: “Eh” Sai na karanta Suratu Nisa’i har na zo wannan aya: “To yaya idan Mun zo da shaidu daga dukan al’umma, kuma Muka zo da kai a kan waxannan kana mai shaida.” (Nisa’i: 41). Sai ya ce: “Ya isa haka.” Sai na juya gare shi, sai ga idanuwansa (SAW) suna zubar da hawaye.” (Buhari ya ruwaito).
Annabi (SAW) ya kasance mafi kamalar halitta wajen ambaton Allah, maganganunsa duka sun kasance zikiri ne ko abin da ya yi kama da shi, haka umarni da haninsa shari’a ne ga al’ummarsa, shirunsa da murmushinsa zikiri ne, zikiri yana gudana ne tare da gudanar numfashinsa (SAW), yana tsaye ko a zaune ko a kinshigixe, haka a tafiyarsa da ruku’insa da hawansa da saukarsa da hutawarsa da zamansa a gida. Ya zo a Sahihu Muslim daga A’isha (RA) ta ce: “Annabi (SAW) ya kasance yana ambaton Allah a kowane lokacinsa.”
Haka sahabbansa (SAW) sun kasance suna son majalisin zikiri, zukatansu suna cika da hawaye, suna kwaxayin yin zikirori na Sunnah, suna sanin ma’anoninsu. Misali babban sahabin nan Al-Irbad bn Sariyya (RA) wata rana bayan Sallar Asuba ya yi wa’azi, wa’azi mai ratsa jiki da idanuwa suka zubar da hawaye zukata suka kaxu sosai…” Tirmizi ya ruwaito.
Allah Maxaukaki Ya ce: “Abin sani kawai, muminai su ne waxanda suke idan an ambaci Allah, zukatansu su firgita, kuma idan an karanta ayoyinSa a kansu, su qara musu wani imani, kuma su ga Ubangijinsu suke dogara.” (Anfal:2).
Kuma Allah Maxaukaki Ya ce: “…Kuma ka yi bushara ga masu qanqantar da kai. Waxanda suke idan an ambaci Allah sai zukatansu su firgita da masu haquri a kan abin da ya same su, da masu tsayar da Sallah kuma suna ciyarwa daga abin da Muka azurta su.” (Hajj:34-35).
Kuma Maxaukaki Ya ce: “Allah Ya sassaukar da mafi kyaun labari, Littafi mai kama da juna, wanda ake kokkoma karatunsa, fatun (jikuna) waxanda ke tsoron Ubangijinsu suna takura saboda shi, sa’annan fatunsu da zukatansu su yi taushi zuwa ga ambaton Allah. Waccan ita ce shiryarwar Allah, Yana shiryar da wanda Ya so game da ita. Kuma wanda Allah Ya vatar, ba ya da wani mai shiryarwa.” (Zumar: 23).
Sheikh Ibn Taimiyya (Allah Ya yi masa rahama) ya ce: “Abin da ke faruwa a lokacin zikiri shar’antacce na kuka da firgitar zuciya da taushin fatu, yana daga cikin falalar da Littafi (Alqur’ani) ya zo da ita.”
Allah Maxaukaki Ya faxi a kan annabawanSa masu girma cewa: “Idan ana karanta ayoyin Mai rahama a kansu, sai su faxi suna masu sujada kuma masu kuka.” (Maryam: 58).
Waxannan idanuwa masu jin zafi idan suka kasance masu zubar da hawaye masu kuka, to lallai wuta ba ta shafarsu kamar yadda Mai gaskiya abin gaskatawa (SAW) ya bayar da labari. Tirmizi da wasu sun ruwaito haka.
“Mutum bakwai Allah zai sanya su a inuwarSa a ranar da babu wata inuwa sai taSa” daga cikinsu. “Akwai mutumin da ya tuna Allah yana shi kaxai, idanuwansa suka zubar da hawaye.” Buhari da Musulim suka ruwaito.
Domin haka idan ka yi zikirin da Annabi ya shar’anta, kuma zuciya ta girgiza ta zubar da hawaye, to madallah da idanuwanka, idanuwa ne da wuta ba za ta shafe su ba da izinin Mabuwayi Mai gafara.
Sirrin da yake cikin haka shi ne lallai wanda ya yi kuka, kuka na gaskiya a lokacin da yake kaxaice, zai yi wuya ya auka wa abin qi, kuma a duk lokacin da ya aikata wani laifi, zai koma ya bi bayansa da kyakkyawa. Allah Ta’ala Ya ce: “Lallai ne ayyukan qwarai suna kore munanan ayyuka. Wancan ne tunatarwa ga masu tunawa.” (Hud:114).
Haqiqa mu muna kukan bushewar zukatanmu da sandarewar hawayenmu da shagaltuwa da laifuffukan waxansu maimakon laifuffukanmu.
Wani mutum ya kai kukan bushewar zuciyarsa ga Hasanul Basri (Allah Ya yi masa rahama), sai ya ce: “Ka horar da ita da ambaton Allah.”
Wanda duk ya yawaita shagaltuwa da duniya, ya qara himma a kanta, ya turke jikinsa da ita, zai hana harshensa ambaton Allah, ya yi tabaibayi ga gavvansa daga yi wa Allah xa’a, zuciyarsa ta kasance a kowane bigire a wofance, rayuwarsa ta kasance cikin shagulgula. Allah Maxaukaki Ya ce: “Kada ku kasance kamar waxanda suka mance da Allah, sai Ya mantar da su kawunansu.” (Hashri:19).
Manzon Allah (SAW) ya ce: “Babu wata sa’a da za ta gushe ga xan Adam a ce bai ambaci Allah ba, face ta kasance baqin ciki a gare shi a Ranar Qiyama.”
An karvo daga Abu Huraira (RA) cewa, lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Mutane ba za su zauna a wani wurin zama ba, a ce ba a ambaci Allah a cikinsa ba, face ya kasance tasgaro a gare su. Kuma babu wani mutum da zai yi tafiya a kan wata hanya amma bai ambaci Allah ba, face hakan ya kasance tasgaro a gare shi, kuma babu wani mutum da zai kwanta a gadon barcinsa bai ambaci Allah ba, face ya kasance tasgaro a gare shi.” Ahmad ya ruwaito.
Zikiri ko ambaton Allah rayarwa ne ga zukata da tsarkake rai da kange bawa daga savo da yin guduma ga Shaixan da yin qaimi ga gavvai wajen yin xa’a ga Allah. Allah Maxaukaki Ya ce: “Ya ku waxanda suka yi imani! Ku ambaci Allah, Ambato mai yawa.” (Ahzab: 41).
Ku ambaci Allah da harshe da zuciya da gavvai, harshe ya jiqa da zikiri, zuciya ta jawu zuwa ga taddaburi da tunani, gavvai su nutsa wajen yin ayyukan xa’a a voye da bayyane. Ba zikiri ba ne mutum ya himmatu da harshensa amma zuciyarsa tana ci gaba da aikata zunubi, ko ya riqa sunkuyar da kai ba tare da kushu’i ga Masanin voye ba. Mene ne amfanin motsa levva da haqora alhali hakan ba ya tasiri a cikin zuciya?