✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zazzabin Lassa ya yi ajalin mutum 37 a Najeriya – NCDC

Mutum 244 aka tabbatar da sun kamu da cutar a fadin kasar nan.

Cibiyar Yaki da Yaduwar Cututtuka a Najeriya (NCDC) ta ce zazzabin Lassa ya yi ajalin mutum 37 a fadin kasar.

Darakta-Janar na hukumar, Dokta Ifedayo Adetifa, ya ce mutum 244 aka tabbatar sun kamu da zazzabin a tsakanin jihohi 16 har da Abuja.

“Bincike ya nuna Najeriya na fuuskantar hatsari game da cutar musamman idan aka yi la’akari da yadda yaduwar cutar ta karu idan aka kwatanta da shekarun baya,” in ji shi.

NCDC ta ce jihohin da aka samu bullar cutar sun hada da Ondo mai mutum 90 da Edo mai 89 da Bauchi mai 13 da Taraba mai mutum 10 da mutum 9 a Binuwai 9, sai kuma mutum 9 a Ebonyi.

Sauran su ne; Nasarawa – 7 da Filato – 5 da Kogi – 4 da Anambra – 2 da Delta – 1 da Oyo – 1 da Adamawa – 1 da Enugu – 1 da Imo – 1 da kuma Abuja – 1.

“Daga cikin ma’aikatan jinya biyar da suka kamu da cutar, guda ya riga mu gidan gaskiya,” in ji Adetifa

(NAN)