Kwamishinar Lafiya ta Jihar Edo, Farfesa Obehi Akoria, ta ce mutum 10 sun mutu tun bayan bullar Zazzabin Lassa a jihar.
Da take zantawa da manema a Benin, babban birnin jihar, Akoria ta ce adadin wadanda suka kamu da cutar a jihar ya karu zuwa 97.
- Kotu ta soke zaben Adekele a matsayin Gwamnan Osun
- Sau 66 muna dakile yunkurin yi wa taron Majalisar Zartarwa kutse —Pantami
Ta ce daga cikin wannan adadi, “Etsako ta Yamma na da 38, Esan ta Yamma 24; Esan Arewa maso Gabas 19; Esan ta Tsakiya 3.
“Esan ta Kudu maso Gabas 2; Etsako ta Gabas 2; Owan ta Gabas 2; Akoko Edo 2; Ovia ta Arewa maso Gabas 2; Oredo 2; sai kuma Etsako ta Tsakiya 1,” in ji shi.
Ta ce gwamnatin jihar ta dauki ingantattun matakai domin yaki da yaduwar cutar a jihar baki daya.
(NAN)