✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zazzabin Lassa ya kashe mutum 142 a Jihohi 23

An gano mutum 142 da suka mutu a jihohi 23 na kasar nan.

Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya (NCDC), ta ce a cikin kasa da wata uku an samu mutum 784 da suka kamu da cutar zazzabin Lassa, yayin da mutum 142 daga Jihohi 23 suka mutu.

NCDC ta wallafa hakan ne a shafinta na intanet, inda ta ce an samu bullar cutar daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa yau.

NCDC ta ce a cikin mako na 11 na annobar, adadin sabbin wadanda aka tabbatar sun warke daga cikin mutum 70 a mako na 10 na 2023 zuwa 38.

An samu rahoton bullar cutar a jihohin Edo, Ondo, Ebonyi, Bauchi, Taraba, Benuwai, Ribas, Filato da kuma Nasarawa.

NCDC ta ce an samu rahoton mutuwar mutum 142.

NCDC ta ce jihohi 23 sun samu akalla mutum guda da aka tabbatar a kananan hukumomi 97.

Ta ce kashi 71 cikin 100 na wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar sun fito ne daga Jihohin Ondo, Edo da Bauchi yayin da kashi 29 cikin 100 suka fito daga Jihohi shida.

A cikin kaso 71 cikin 100, Ondo na da kaso 32, Edo 29 sai Bauchi mai kaso 10.

A cewar NCDC, yawancin shekarun wadanda suka harbu da cutar bai gaza 21 zuwa 30 ba.

Kazalika, NCDC ta ce wani ma’aikacin lafiya ya kamu da cutar a mako na 11.