An shiga cikin zullumi bayan cutar Zazzabin Lassa ta kashe mutu hudu, ciki har da likitoci biyu da wata mata da karamin yaro a Jihar Nasarwa.
A makon jiya ne Aminiya ta kawo rahoton da Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nasarawa ta sanar da sake samun bullar cutar mai kisa a jihar.
- Daga Laraba: Illolin da rashin kaunar juna ke yi wa mata
- An samu bullar Zazzabin Lassa a Jihar Nasarawa
A ranar Juma’a ce Babbar Sakatariyar Ma’aikatar, Dokta Janet Angbazo, ta ce “An tabbatar da kamuwar mutum biyu, akwai wasu uku kuma da ake zargi sun harbu da cutar kuma ana lura da su a cikin jihar nan.”
Da take sanar da haka ranar Juma’a, ta bayyana cewa an dauki samfurin jinin karin wasu mutane da ake zargi da kwayar cutar zuwa dakin gwaje-gwajen Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Kasa (NCDC) domin tantancewa.
— Alamomin cutar Zazzabin Lassa
“Alamomin cutar sun hada da zazzabi na mako daya zuwa mako uku bayan kamuwa da kwayar cutar.
“Kashi 80 cikin 100 na alamomin cutar Lassa ba su bayyana ta yadda za a iya gane su.
“Kashi 20 cikin 100 na masu cutar na iya fama da zazzabi mai tsanani, sarkewar numfashi, amai, jijjiga, kumburin fuska, da kuma ciwon kirji da baya da mara.
“Cutar na iya yin kisa a sakamakon daina aikin wasu sassa na jikin dan Adam,” kamar yadda ta bayyana.
Don haka ta shawarci jama’ar jihar da su dauki kwararan matakan kariya ta hanyar nisantar masu cutar gami da tabbatar da tsaftar muhalli domin kawar da beraye da dangoginsu.