Wani binciken shirin dakile cutar zazzabin cizon sauro a Najeriya ya gano cewa akalla mutum daya ne ke mutuwa sakamakon kamuwa da ciwon duk cikin minti daya a kasar.
Da yake jawabi a ranar zazzabin cizon sauro ta duniya, Kwamishinan Lafiya na Jihar Adamawa, Abdullahi Isa, ya ce mutum 90,000 da suka mutu a Najeriya na da alaka da zazzabin cizon sauro a duk shekara.
- Sojoji sun kashe mayakan ISWAP 26 a Borno
- Tarayyar Afirka ta taya Macron murnar sake lashe zaben Faransa
Kwamishinan ya yi gargadin cewar cutar na daga cikin manyan cututtukan da suka addabi duniya, musamman ma Afrika.
Ya ce “A baya-bayan nan, binciken shirin dakile cutar zazzabin cizon sauro, ya bayyana yadda mutum 90,000 suka mutu sakamakon cututtukan da ke da alaka da zazzabin cizon sauro a Najeriya.
“Mutum tara cikin 10 na ’yan Najeriya na mutuwa ne a sakamakon kamuwa da zazzabin cizon sauro a kowane awa daya,” inji Kwamishinan.
Sai dai ya bayyana yadda aka samu ci gaba inda cutar ta sami koma-baya daga kashi 27 cikin 100 a 2015 zuwa kashi 23 a 2018.
Har wa yau, ya ce za a iya shawo kan kamuwa da cutar ta hanyar bai wa yara ’yan kasa da shekara biyar a duniya kulawa ta musamman.
“Adamawa na bakin kokarinta wajen ba da tallafin da ya dace don yaki da zazzabin cizon sauro,” a cewarsa.