A ranar Asabar 17-04-1441 Bayan Hijira, daidai da 14-12-2019 (Miladiyya) Gizagawan Najeriya suka hallara a zauren taro na Sultan Sa’ad Abubakar da ke Kwalejin Barewa, Zariya, Jihar Kaduna, inda suka gudanar da taronsu na bana, wanda shi ne karo na 6 tun kafuwar kungiyar. Babban Bako Mai Jawabi, Farfesa Ibrahim Aliyu Muhammad Malumfashi, na Jami’ar Jihar Kaduna, ya samu wakilcin Dokta Ibrahim Shehu Liman (08023703718), shi ma na Jami’ar Jihar Kaduna, wanda kuma ya samu gabatar da mukala mai taken “Gudunmawar ’Yan Jarida Ga Rayuwar Al’umma.”
Shugabanni da manyan baki, ’yan jarida, ’ya’yan Kungiyar Gizago da sauran jama’a, assalamu alaikum.
Ina cike da farin ciki dangane da wannan gayyata da kuka yi mini a babban taron kungiyarku ta Gizago. Akwai muhimman abubuwa uku da ya kamata mu yi sharar fage a kansu, kafin tattauna batun da aka tsara cewa shi ne alkiblar wannan taro.
Wadannan abubuwa su ne, ita kanta Kungiyar Gizago, marigayi Alhaji Mahmoon Baba Ahmad da kuma halin da ake ciki da ke matukar bukatar irin wannan taro.
Dangane da taken wannan taro, “Gudunmawar ’Yan Jarida Ga Rayuwar Al’umma” lallai wadanda suka yi tunani kan haka sun yi hangen nesa. Da farko dai akwai bukatar waiwayen ko wane ne dan jarida da irin aikin da ke gabansa, sannan a waiwayi ita al’umma, misali Hausawa domin ganin yadda aikin ’yan jarida ke bayar da gudunmawa ga rayuwarsu.
Tarihin aikin jarida
Current, R. N. da wadansu (1965) sun ce aikin jarida ya samo asali ne daga irin labaran da fatake da sauran matafiya kan rika bazawa tun kafin a fara samun takardu da za a rubuta ko daga baya a buga. Irin wadannan labarai ba su da madogara sosai, akwai kare-karen gishiri da rashin tabbaci.
A 1556, gwamnati a kasar Amurka ta rika samar da ’yan takaitattun labarai da ake rubutawa da hannu a takardu. Irin wadannan labarai sun shafi bayanai dangane da siyasa, sha’anin tsaro da ke da alaka da ayyukan soji da tattalin arziki. Daga baya, a wajajen 1601, an fara samun aikin dab’i wanda ya yi sanadiyyar samuwa da bazuwar jaridu a kasashen Turai, musamman a Amurka, Ingila, Faransa, Spain da Italiya. Ana kiran irin wadannan jaridu da sunan ‘relations.’ Haka abin ya yi ta bunkasa da watsuwa har aka samu abin da ake kira da jaridu, mujallu da sauran kafafen watsa labarai da suka hada da radiyo da talabijin.
Mene ne aikin ’yan jarida?
Aikin jarida kamar yadda Dodge, J. D da Biner, G. (1963) suka bayyana, ya kunshi tattara bayanai, rahotanni da gundarin labarai domin bayyana manufofin hukuma, fadakarwa da wayar da kai da kuma ilimantar da jama’a kan abubuwan da suka shafi baki dayan rayuwa, musamman tsare-tsare da manufofin hukuma, kamar abubuwan da suka shafi siyasa, mulki, tsaro, tattalin arziki da makamantansu. Haka wadannan kafafe na watsa labarai sukan samar da damar nishadantar da jama’a da tallata hajoji.
Mene ne labari?
Kamar yadda masana da wadanda suka goge a fannin aikin jarida suka bayyana, labari shi ne duk wani abu sabo da aka bayyana, koda kuwa a hakikani abin a kashin kansa ba sabo ba ne, amma labarin da aka bayar wanda ya dangance shi sabo ne. Ana iya samun labari daga bakin jama’a, kamar fatake ko wadansu da suka zama jiyau ko jiyau sannan ganau. A zamanance, akwai kafofin watsa labarai da dama wadanda suka hada da gidajen rediyo da talabijin da jaridu da mujallu da hanyar sadarwa ta Intanet da makamantansu.
A fagen aikin jarida, akan tattara labari ne a rubuce ko a dauka a rikoda ko kyamara, wani lokaci kuma yana iya kasancewa a bayyane ne ake bayar da shi.
Masu samar da labarai, wato ’yan jarida kan bayyana labarai ne bisa gaskiyar hakikanin abin da suka binciko suka kuma tantance. Duk labarin da ya saba wadannan matakai, ya zama kanzon kurege, wato abin da ake kira ‘junk’ da Ingilishi.
Yaya aikin jarida ke zama nagartacce?
Aikin jarida kan zama nagartacce ne idan ana bin tanade-tanaden aikin, kasancewar duk abin da aka ce labari ne daga wata kafar watsa labarai, ana sa rai ya zama amintacce.
Breytenbach, B. (1983) shi ma ya bayyana cewa kowane marubuci dan rahoto ne, kuma mai bin kwakkwafi da bayyana abubuwan da ke faruwa a cikin al’umma. Tanade-tanaden aikin dan jarida sun hada da:
1-Yin bincike na hakika ko tattaro labarai daga amintattun madogarai.
2-Tace duk labarin da ake son watsawa ga jama’a.
Akwai kuma wasu muhimman ginshikai da suke yi wa masu aikin jarida jagora wajen gudanar da aikinsu. Sun kuwa hada da:
1-Kwarewa a fagen aikinsu ta hanyar yin karatun aikin a matakai daba-daban a manyan makarantu.
2-Halartar kwasa-kwasai domin samun kwarewa.
3-La’akari da al’adu da tarbiyya da kuma tsarin rayuwar al’umma.
4-Taka-tsantsan da duk abin da zai zama barazana ga zaman lafiya da sauransu.
5-Samun kwarewa ta hanyar dadewa da kuma samun jagororin aiki nagari.
Gudunmawar aikin jarida ga al’umma (Hausawa)
Masana da dama da suka hada da Boston, R.(1970) da Whale, J. (1972) sun bayyana aikin ’yan jarida da cewa ya hada da:
1-Ilimantarwa a fannonin rayuwa daban-daban.
2-Wayar da kai dangane da manunfofin Gwamnati.
3-Karewa da bunkasa al’adu. 4-Karewa da bunkasa harshe. 5-Karewa da bunkasa addini. 6-Bunkasa harkokin tattalin arziki. 7-Kyautata jiyayya da tabbatar da tsaro.
8-Shawo kan fitinu da bala’o’i. 9-Shawo kan cin zarafi ko muzgunawa ko gallaza wa jama’a.
10-Kyautata walwala da ’yanci. 11-Sanin yanayi, hali da ci gaban da ake samu a wasu sassa ko ma duniya baki daya.
Alhakin gwamanti gangane da kafafen watsa labarai
1-Bayar da ’yanci ga kafafen watsa labarai da ma’aikatansu. 2-Yin linzami ta hanyar samar da manufofin kyautata aikin jarida. 3-Samar da dokoki da kafa hukuma da za ta sanya ido ga kafafen labaran da ke kokarin wuce gona-da-iri, ta hanyar harzuka jama’a da ruruta fitina ko yin kafar ungulu ga gwamnati (inda take da manufofi masu amfani ga jama’a) ko makarkashiya ga ita gwamnatin da al’umma.
Kalubalen da ke fuskantar kafafen watsa labarai
1-Bukatar samar da nagartattun tsare-tsaren gudanarwa. 2-Kayan aiki wadatattu kuma wadanda suka dace, kamar takardu, rukodoji, kyamarori, makirfo, kwamfutoci da ababen hawa. 3-Samar da ofisoshi da kayan dab’i. 4-Samar da hanyoyin Intanet da hanyoyin tattara labarai da bayanai na zamani. 5-Samar da dakunan karatu (laburare) tare da tanadar muhimman littattfai da mujallu da dukkan abubuwan da za su taimaka wajen samar da bayanai na hakika da kuma adana su. 6-Samar da ma’aikata a matakan da suka dace, kamar masu farauto labarai da rahotanni a fagage irin na tsaro, kiwon lafiya, ilimi, tattalin arziki, noma da kiwo, masana’antu, kimiyya, siyasa, fasaha, sha’anin mulki, labaran kasashen waje, wasanni da matasa; haka kuma wajibi ne a samar da masu tace labarai da sauransu. 7-Bayar da dama ga ma’aikatansu domin su rika samun horo na kwarewa a-kai-a-kai. 8-Biyan ma’aikata albashi da alawus-alawus da suka dace. 9-Karramawa da kyautata jin dadin ma’aikata. 10-Ladabtarwa ga duk ma’aikacin da ke saba ka’idoji da sharuddan aiki.
Kalubalen da ke fuskantar ’yan jarida dangane da aikin da suke yi wa jama’a:
1-Samun kwarewa a fagen aikinsu. 2-Kauce wa yada fitina da tayar da husuma. 3-Bin dokoki da ka’idojin aiki. 4-Jajircewa wajen yi wa al’umma aiki. 5-Samar da kungiya ko wata mahada, wato cibiya da za ta rika sanya ido kan ci gabansu da dakile ayyukan bata-gari a aikin. 6-Kyautata jiyayya da hukumomi da kuma jama’a. 7-Tsayawa ga halal da kauce wa kwadayi (sanin darajar kai).
Kammalawa:
Daga bayanan da suka gabata, mun gano cewa dan jarida mai bincike ne da bin kwakkwafi tare da bayar da rahoto dangane da abubuwan da ke faruwa a cikin al’umma. Haka nan, shi ke hangowa, sannan ya yi hasashen mafita kan wasu matsaloli, ko bayar da shawarwari kan yadda za a kyautata da bunkasa wasu harkokin rayuwar jama’a.
A karshe, ga hannunka mai sanda ga ’yan jarida da duk masu aikin da ya danganci aikin jarida, musamman marubuta littattfai da marubuta a jaridu da mujallu. Shin ko suna taimakawa wajen karewa, bunkasawa da yada harshe da al’adun Hausawa? Ko suna bayar da irin wannan taimako ta fuskar tattalin arziki, siyasa, tsaro da sauran fannonin zamantakewar al’ummar Hausa? Idan ana samun haka, to, tubarkalla, idan kuwa akasin haka ne, to da sake ke nan.